Kwamishanan ilimi na jihar Alhaji Musa Inuwa Kubiyo ne ya bayyana hakan a wata firar da ya yi da wakiliyar Muryar Amurka Sa'adatu Fawu. Ya ce sun yi wasu abubuwa a makarantu da suka jawo hankalin iyaye lamarin da ya sa suka soma dawo da 'ya'yansu makaranta. Da sai iyaye sun tallafawa 'ya'yansu amma yanzu gwamnati ta dauki nauyinsu dari bisa dari. Gwamnati ta gyara gidajen kwana da na daukan darusa da na malamai. Kusan kashi saba'in da biyar bisa dari na tsofofin makarantu aka sabunta. Ban da haka an kuma gina wasu sabbi.
Dangane da ilimin mata kwamishanan ya ce gwamnati ta mayarda hankali kan iliminsu. A wasu makarantun ma mata sun fi yawa. Amma akwai wasu sassa na jihar inda har yanzu ilimin boko nada koma baya domin gurguwar fahimta da aka yi ma ilimin. Bugu da kari wadanda suka anfana da ilimin boko daga wadannan sassan basu koma wuraren nasu ba yadda mutanensu zasu yadda da su su faminci alfanun ilimin. Sabo da haka gwamnan jihar zai kafa wani kwamiti na musamman ya zagaya wadannan sassan ya wayar wa mutanen wurin kawunansu a kuma dubi matslarsu. Ya ce a zahiri gaskiya akwai rashi wanda damuwa ne domin suna anfani da 'ya'yansu wurin biyan bukatunsu na yau da kullun. Yanzu gwamnati zata biya ma iyayen bukatunsu domin su bar yara su je makaranta. Misali kowane uba ya kai dansa makaranta za'a bashi tallafi domin ya bar dansa ya cigaba da makaranta. Su kuma yaran za'a ciyar dasu a makarantu a yi masu sutura a kuma kula da lafiyarsu. Idan kuma zasu cigaba da karatunsu gwamnati zata dauki nauyinsu.