Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wadansu Kungiyoyin Matasan Arewa Sun Goyi Bayan Kungiyar Dattawan Arewa


Matasa a arewacin Najeriya
Matasa a arewacin Najeriya

Yunkurin da kungiyar dattawan arewa ke yi na gurfanar da Janaral Ihejirika gaban kotun kasa da kasa bisa ga zargin cin zarafin 'yan Najeriya musamman a arewa maso gabashin kasar ya samu goyon bayan kungiyoyin matasan arewa masu zaman kansu.

Kungiyar Dattawan Arewa ta samu goyon bayan kungiyoyin matasan arewa domin hakarsu ta cimma ruwa.

Imranu Wada Nas shugaban kungiyar inganta rayuwar matasan arewa ya ce karar da za'a kai Janaral Ihejirika a kotun kasa da kasa ba guda ba ce. Bayan dattawan sun kai tasu su ma matasan arewa zasu kai tasu karar domin su tabbatar da cewa gaskiya ta tabbata kuma an yi masa hukuncin da ya kamata a yi mashi domin zaluncin da ya yi na rashin kyautawa da ya yi da kuma son zuciya na bangaranci. Ana samun tashin hankali a wurare da dama to amma a ina aka taba zuwa aka yi irin rashin mutunci da Janaral Ihejirika ya yi. Ya ce dalili ke nan da suke kuka da manyansu domin sun yi shiru basa magana. Ya ce amma yanzu sun godewa Allah domin hankalin dattawan ya dawo sun gane bakin cikin da suke ciki tun da can. Domin haka suna goyon bayansu dari bisa dari. Kuma bayan sun gama tasu su ma zasu kai tasu karar.

Kungiyar Network For Justice Malam Aminu Sule ya ce kungiyarsu na goyon bayan duk wani yunkuri da za'a yi na kare hakin bil adama. Ya ce duk wani abu da zai kare hakin mutum kungiyarsu na farin ciki da shi kuma suna goyon bayanshi. Sabili da haka duk keta hakin bil adama da aka yi a bincikesu a kuma hukunta wanda aka samu da laifi. Lokacin sojoji haka suka rinka fama da su dangane da keta hakin jama'a da suka dinga yi. Sun kaisu kotu inda kuma ya kamata su wayar da kawunan mutane sun yi. Burinsu shi ne kasar Najeriya ta zama tana da matsayi wurin kare hakin bil adama kamar yadda dokokin duniya suka tanada.

Amma Mark Amali na kungiyar Middle Belt Forum ya ce duk tarurukan da dattawan arewa ke yi basu cika gayawa juna gaskiya ba sabo da haka shi baya goyon bayansu. Ya ce yana kiran wadanda suke kiran kansu dattawan arewa idan za'a yi taro su kira kowa da kowa kuma kowa a bari ya fadi ra'ayinsa. Ya ce idan shi yanzu ya je taron idan dai ba wai za'a yi anfani da shi ba to ba za'a bari ya yi magana ba ko ya fadi ra'ayinsa ba. Zamansu sai dai idan zasu zalunci jama'a. Idan ba za'a zauna a gyara ba a nemi ra'ayin kowa da kowa to taron banza ne. Idan ba za'a fito a fadawa juna gaskiya ba zancen banza suke yi. Wai yaudarar mutane suke yi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG