Janaral Buhari ya ce anfani da karfin soji ba zai haifi da mai ido ba. Hanyar hawa teburin sulhu ita ce kadai hanyar da zata kaiga zaman lafiya. Ya ce a koma aikin kare kasa yadda ya kamata. Sojojin da suke aiki yanzu abun da ake zargin 'yansanda da yi suma suna yi yanzu. Idan mutum ya zo wani zibin sai a tsareshi sai ya bada kudi kafin ya wuce. Da ba'a san soja da yin haka ba. Haka kuma sojoji na shiga gidajen mutane suna cin mutuncin maza gaban iyalansu. Wani lokacin ma a yiwa matansu fyade gaban mazansu kamar abun da ya faru a Baga. Ya ce idan an kashe soja daya ko biyu duk garin kuma sai an kashe kowa da kowa.
Ya ce wace gwamnati ce zata zuba ido ana kashe al'ummarta? Ya bada misali da 'yanbindigan Neja Delta. A lokacin marigayi Shehu 'Yar'adua aikawa ya yi da jirgi aka dauko shugabannin 'yan tawayen ya lallashesu kana ya basu kudi aka yi masu tsarin koya masu ayyuka kana suka dawo aka basu ayyuka. Amma na Boko Haram da suka fara me a ka yi masu? Kashesu a ka yi.Da 'yansanda suka kasa aka kawo sojoji su suka kamo shugabansu Mohammed Yusuf kana suka mika shi ga 'yansanda. Haka ake aikin tsaro. Hakin 'yansanda ne su kwantar da tarzoma idan suka kasa sai a tura soja. Su kuma soja ba wai su kashe duk wani abu mai motsi ba.
Kalamun na Janaral Buhari na zuwa ne yayin da wasu kananan sojoji dake Monguno ke korafin an yi watsi dasu tun shekarar 2012. A bayansu an kawo wasu sun gama kuma an mayarda su amma nasu lamarin shuru kake ji kamar an shuka dusa.