Alhaji Gambo yace “a yau Talata, hudu ga watan biyu, shekara ta 2014, ni Gambo Sallau, shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano, na sauka daga wannan mukamin, saboda dalilai na siyasa. Ba zan iya komawa wata jam’iyya daga jam’iyyata, ta PDP ba.”
“Ina so in yi amfani da wannan dama, in yi wa Allah (S.W.T) godiya, saboda dama da Ya bani, don in jagoranci majalisar dokokin jihar Kano na shekara biyu da wata biyu. Allah Ya bani dama na jagorance ta cikin nasara. Ina yiwa abokan aiki na, na majalisar dokokin jihar Kano godiya, saboda hadin kai da goyon baya da suka bani a lokacin da nake jagorantar su.” A cewar tsohon shugaban.
Tuni dai wakilan majalisar suka zabi mataimakinsa Honorable Isiyaku Ali Danja, a matsayin sabon shugaban majalisar, yayinda aka zabi tsohon shugaban masu rinjaye Honorable Hamisu Ibrahim a matsayin maimakin shugaba.
Litininnan da ta wuce ne wakilai 27 na jam’iyyar PDP a zauren majalisar sukayi sauyin sheka zuwa jam’iyyar APC lamarin da saka adadin ‘ya’yan APC a zauren majalisar ya kai 34 yayinda PDP ke da 6.