A wata muhawa mai zafi, da yawanci ‘yan jam’iyyar adawa ta APC suka nuna rashin gamsuwarsu, ‘yan jam’iyyar PDP mai mulki na goyon bayan dokar.
Ganin yadda muhawara ta kasance a majalisar ne yasa wakiliyar Muryar Amurka Madina Dauda ta tambaye Hadi Suleika daga jihar Katsina akan ko zasu iya bin umarnin jam’iyyar APC kuwa ganin cewa yanzu ba sune suke da rinjaye ba.
Hadi Suleika yace “babu ma yadda za’a yi a tattauna wannan kasafin kudi na bana, saboda akwai abubuwan da ba’a kawo ba, wadanda ya kamata a kawo su tare da kasafin kudi kamar abubuwan da suka jibanci yadda ake samo kudin ma su shigo Najeriya kafin a kasafa su, sai an fada. Da yadda za’a kashe kudin, da yadda za’a tsara su. Duk wannan sai an yi bayani filla filla tukunna kafin a kawo.”
Sai dai Abdulmumini Hassan PDP Jigawa yace ba zai yiwu a ce babu wani abu mai amfani a cikin kasafin kudin ba. Yace “Ina tabbatar da cewa, duk wadannan abubuwan, baka cewa an yi katon littafi irin wannan, wajen littatafai guda uku, kace babu komai wanda zai amfani mutane. Kawai abinda za’a iya cewa shine akwai wuraren da yakamata a ce an fi bawa muhimmanci, ba’a basu ba.”
A halin yanzu, majalisar dattawa ta mayar da kundin kasafin kudin ga kwamitin kula da kasafin kudi.