Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Zaman Lafiya Ta Duniya: An Nemi Hanyar Dakile Matsalar Tsaro a Borno


An gudanar da taron karawa juna sani tare da tuntuba a jihar Borno inda ake fama da matsalar tsaro, yayin kiyaye ranar zaman lafiya ta duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ware wannan rana da nufin ganin an sami zaman lafiya a ko'ina a duniya ko da kuwa na wuni guda ne. Ta haka ta nemi a ware akalla sa'o'i 24 don tsagaita wuta a dukan inda ake fadace fadace da ake da ya zamo ranar da babu fada a duk fadin duniya.

Akan tattauna matsalolin tsaro ne a irin wannan rana a duk fadin duniya ciki har da Najeriya, musamman ma a Borno dake arewa maso gabashin kasar, data samu kanta cikin iftila’in rashin tsaro sanadiyar hare -haren boko haram da suka addabi yankin.

A bukin na bana, wata kungiya da ake kira “Ambassadors of Peace,” wato jakadun zaman lafiya, ta kira taron hadin kai da jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki akan harkar tsaro dama majibancin harkokin yau da kullun don tattauna hanyoyin da za’a bi wajen magance wannan matsalar tsaro da aka shafe shekaru 11 ana fama da shi.

A hirar shi da Muryar Amurkar, Ambassador Ahmed Shehu shugaban wannan kungiyar ya bayyana cewa, galibi rashin aikin yi da zaman kashe wando musamman tsakanin matasa ne ke cusa da dama cikin ayyukan ta'addanci da tada zaune tsaye. Yace, “akwai matasa masu karfi da basu da aikin yi, saboda haka duk mai so ya samu na cin abinci idan ya rasa, aka zo musu da da wannan magana dole ya bi"

Wadanda suka gabatar da kasidu a taron sun hada da Alhaji Umaru Bako, da kuma Professor Khalifa Dikkwa Malamai a Jami’ar Maidugu, wadanda suka kara jadada samarwa matasa ayyukan yi da kuma kara sa ido kan masu tsatsauran ra'ayi.

Saurari cikakken rahotan Haruna Dauda Biu daga Maiduguri:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG