Baya ga sanarwar da aka danganta da hukumar hana fasakwauri na kwastam a kan ayyukan mayakan boko haram a birnin Abuja da kewaye, ‘yan bindiga dadi sun kai hare-hare a kauyen tungan maje inda suka yi garkuwa da mutane da dama, hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka harbi mutane da dama da ya hada da wani dan jarida da ke aiki da tashar NTA a jihar Nassarawa.
Wani ganau da ya bukaci a sakaya sunansa a kauyen Tungan Maje ya bayyana cewa, ‘yan bindigan sun afkawa al’umman yankin ne da misalin karfe 1 da minti 10 na dare inda suka yi ta harbi, suka shiga gidajen mutane tare da kwashe kayan abinci da kudade kuma suka yi awon gaba da mutane 12, suka tafi da su cikin daji amma daga baya suka saki mutane biyar da suka hada da dattawa.
Majiyoyi daga jihar Kaduna sun bayyana cewa, ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun yi awon gaba da ‘yan gida daya 17 a yayin da suke kan hanyar zuwa gona tare da jikkata sauran ‘yan uwan hudu a kauyen Udawa dake karamar hukumar Chikun Na jihar.
Wani shugaban al’umma a kauyen Udawa, Liman Hussaini, ya bayyana cewa, yan bindigan sun afka mu su a ranakun juma’a da asabar inda suka yi garkuwa da mutane da dama.
A jihar Ekiti ma, da safiyar ranar litinin ne ‘yan bindiga suka far wa gidan daraktar gudanarwa na ayyukan kananan hukumonin jihar ,David Jejelowo dake unguwar Igirigiri na fadar gwamnatin jihar inda suka kashe shi.
Hukumomin tsaron kasar da suka hada da rundunar ‘yan sanda, rundunar soji, hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS da sauransu sun bayyana cewa suna yin duk mai yiyuwa wajen tsare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra'uf:
Facebook Forum