Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Afirka CAF Issa Hayatou ya rasu. Shekarunsa 77.
Hayatou wanda dan asalin kasar Kamaru ne, ya rasu bayan fama da rashin lafiya.
Hayatou ya taba rike mukamin Shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta duniya FIFA a mataki na rikon kwarya.
“Muna masu alhini da jin labarin rasuwar tsohon shugaban hukumar CAF, tsohon shugaban FIFA na wucin gadi, tsohon mataimakin Shugaban FIFA kuma mamba a majalisar FIFA Issa Hayatou.” Shugaban FIFA Gianni Infantino ya ce a shafin Instagram.
Kazalika mamacin tsohon mamba ne a kwamitin shirya wasannin Olympics shekaru 15 da suka wuce.
Koda yake tsohon dan wasan tsere ne, amma Hayatou ya fito idon duniya ne sanadiyyar wasannin kwallon kafa.
Tsohon dan wasan kwallon Kamaru Samuel Eto'o wanda ya yaba irin rawar da Hayatou ya taka wajen bunkasa sha'anin kwallon kafa a nahiyar Afirka, ya ce Hayatou ya rasu ne a birnin Paris na kasar Faransa.
Dandalin Mu Tattauna