Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fitar Da Rivers United Daga CAF Confederation Cup


'Yan Wasan Kungiyar Rivers United
'Yan Wasan Kungiyar Rivers United

Kungiyar Young Africans ta Tanzania ta fitar da zakarun Najeriya, 'yan kungiyar Rivers United daga gasar CAF Confederation Cup.

‘Yan wasan na tawagar su Stanley Eguma sun tashi babu da babu, wato 0-0 da masu masaukinsu a filin wasa na Benjamin Nkapa da ke Dar es Salam da daren ranar Lahadi.

'Yan Young Africans sun yi nasara a wasan daf da na kusa da karshe da ci 2-0.

An dakatar da wasan bayan an shafe mintuna 24 ana wasan saboda matsalar fitilar filin.

An bai wa kungiyoyin biyu minti 10 su motsa jiki kafin a sake fara wasan.

‘Yan wasan Rivers United sun yi kokari matuka amma sun kasa kutsawa cikin gidan masu masaukin bakin.

Kungiyar Young Africans zata fafata da Gallants ta Afirka ta Kudu a wasan kusa da na karshe.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG