Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Hadarin Jirgin Washington Ya Karu Zuwa 28


Bayan jirgin saman farar hula mai dauke da fasinjoji 64 da kuma jirgin sama mai saukar ungulu na soji sun yi karo a sararin sama sun fado, ana fargabar cewa rayuka sun salwanta.

Shugaban hukumar kashe gobara ta birnin Washington John Donnelly ya shaidawa taron manema labarai cewar adadin wadanda suka mutu a hatsarin jirgin saman ya karu zuwa mutane 28 yayin da ma’aikatan bada agaji, da yawansu ya kai kimanin mutum 300, ke aiki cikin yanayi mai matsanani rashin kyau kuma suna nuna alamun cewar zai yi wuya a samu sauran mai rai.

Wani karamin jirgin saman fasinja dauke da mutane 64 ya rikito cikin kogin Potomac na birnin Washington a jiya Laraba bayan da yayi karo da wani shelkwaftan soja a sararin samaniya, inda kafafen yada labaran Amurka suka bada rahoton tsamo dimbin gawawwaki daga cikin duhun kogin dake da matukar sanyi.

Ana ci gaba da gagarumin aikin ceto, inda masu ninkayar dake nutso cikin kogin Potomac da dusar kankara ta lullube domin tattaro tarkacen jiragen saman 2.

Jirgin kirar bombardier da wani reshen kamfanin sufurin jiragen saman American Airlines ke gudanarwa na tunkarar filin saukar jiragen saman “Reagan National Airport” da misalin karfe 9 dare agogon amurka bayan daya taso daga birnin Wichita na jihar Kansas, sa’ilin da hatsarin ya afku.

Yadda Jirgin Sama Ya Yi Karo Da Jirgi Mai Saukar Ungulu A Washington DC
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p

No media source currently available

0:00 0:32 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG