Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samar Da Fetur A Matatar Dangote Na Shafar Kasuwannin Turai - OPEC  


Matatar mai ta Dangote (Hoto: Facebook/Dangote)
Matatar mai ta Dangote (Hoto: Facebook/Dangote)

OPEC tace sakamakon kokarin da matatar da ke da mazauni a Legas ta ke yi, dole ne tarin man da ake samarwa a kasuwannin duniya ya nemi wasu sabbin kasuwannin.

Kungiyar kasashen masu arzikin man fetur (OPEC) ta bayyana cewa samar da albarkatun man fetur din da matatar Dangote ta ke yi ya rage yawan shigo da albarkatun daga nahiyar Turai.

A cikin rahotonta na wata-wata a kan kasuwar mai da aka wallafa a ranar 15 ga watan Janairun da muke ciki, OPEC tace sakamakon kokarin da matatar da ke da mazauni a Legas ta ke yi, dole ne tarin man da ake samarwa a kasuwannin duniya ya nemi wasu sabbin kasuwannin.

Yanzu matatar man Aliko Dangote da aka gina a kan dala biliyan 20 da ka iya tace ganga 650, 000 a kullum na samar da tataccen dizil da fetur da kuma man jirgin sama ga dillalai.

Najeriya, kasar Afirka mafi yawan jama’a, na fuskantar matsalar makamashi, inda dukkanin matatun man gwamnatin kasar suka daina aiki tsawon lokaci in banda a baya-bayan nan.

Kasar ta dogara ne kacokan a kan shigo da tatattun albarkatun man, inda kamfanin man kasar NNPC ya kasance babban mai shigo da muhimman kayayyakin bukatar.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG