Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Tambayoyi Game Da Yanayin Tsaro A Kasar Mali


Oumar Diarra shugaban sojojin kasar Mali lokacin da ya ke magana da manema labarai a birnin Bamako.
Oumar Diarra shugaban sojojin kasar Mali lokacin da ya ke magana da manema labarai a birnin Bamako.

Babu cikakkun bayanai game da halin da yanayin tsaro ke ciki a kasar Mali a yau Laraba bayan da a jiya Talata wasu masu tada kayar baya suka afkawa kwalejin horas da jami’an ‘yan sanda da wasu muhimman wurare.

'Yan tawayen dai sun hallaka ‘yan sandan dake samun horo tare da kwace wani bangare na filin saukar jiragen sama har ma da cinnawa wani jirgin shugaban kasar wuta.

Harin Mali
Harin Mali

Masu fashin baki da jami’an diflomasiya sun bayyana harin da mummunan koma ga gwamnatin mulkin sojan kasar da kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen afrika ta yamma (ECOWAS) sannan tarayyar Turai ta fitar da sanarwar dake alla-wadai da shi.

Gwamnatin Mali bata tabbatar da adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin ba, sai dai ta bayyana a tashar talabijin kasar da yammacin jiya Talata cewa an samu “wasu” mace-mace.

Mali
Mali

Wani hoton bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna wani dakin kwana dauke da jerin gadaje masu sama da kusan dozen 2 an banka musu wuta. Ana iya ganin gawawwakin da suka kone, wasu a karkashin gadajen. kamfanin dillancin labaran Reuters bai tantance sahihancin bibiyon ba.

MALI
MALI

Da safiyar yau Laraba, an ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama a babban filin saukar jiragen saman birnn Bamako, inda galibin tashe-tashen hankulan da kungiyar Jama’a Nusrat ul-Islam wa al-Musulmin ta yi ikrarin suka faru.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG