Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar Bauchi Ta Nemi Tallafi Bayan Bala'in Guguwa Da Gobara


Barrister M.A. Abubakar, gwamnan jihar Bauchi
Barrister M.A. Abubakar, gwamnan jihar Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi Barrister M.A. Abubakar ya koka da irin bala’in da gobarar kasuwar Azare da guguwa dauke da ruwan sama suka haddasa a jihar.

Aukuwar gobara a kasuwar Azare ta lakume fiye da kashi uku na kasuwar kurmus. A na cikin hakan ne kuma aka samu ambaliyan ruwa wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane takwas a Bauchi.

Gwamnan jihar Barrister M.A. Abubakar ya zagaya domin ya ga irin barnar da ambaliyan ruwan da wuta suka yia a jihar.

Yace ya zagaya garin Bauchi da Darazo, da Misau da kuma Ningi domin ganin jama’a. Yace mutane takwas ne suka rasa rayukansu, kuma bashi da wani cikakken bayani ko cikin wadanda suka ji rauni wani ya rasu”.

Gwamnan yace kasuwar garin Azare kusan kashi uku cikin hudu na kasuwar ta kone kurmus.

Yace gwamnatinsa ta bada taimakon gaggawa na kayayyakin abinci da kuma sutura, kafin a yi kidigdigar hasarar da aka yi saboda samun taimako na mausamman.

Barnar ta fi karfin jihar Bauchi. A saboda haka ya bukaci taimako daga gwamnatin tarayyar Najeriya da kuma masu hannu da su taimakawa al’ummar jihar Bauchi da wannan masifa ta rutsa dasu.”

Yanzu haka dai shugaban ma’aikatan tallafawa wadanda irin wannan bala’I ya rutsa dasu na tarayyar Najeriya yana kan hanyarsa ta zuwa Bauchi . Gwamnan ya kuma baiyana fatar shugaban kasa zai ziyarci jihar domin ganin irin barnar da suka auku.

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya yi al’ummar jihar Bauchi jaje game da wannan abu da ya faru”

Gwamnatin jihar Bauchi ta kafa kwamitin masana akan wannan al’amari.

A saurari gwamnan a wannan rahoton Abdulwahab Muhammad

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG