A jiya Talata ne duka ‘Yan majilisar dokokin Amurka daga dukkan jamiyyu dake majilisar sun amince da su dauki mataki a majilisance domin kawo karshen tsarin nan na raba yara da iyayensu a bakin iyakar Amurtka da Mexico.
Wannan dai Gwamnatin Trump ce ta kirkiro shi wanda kuma ya haifar da damuwa a majilisar dokokin na Amurka.
Babbar darektar hukumar tallafawa yara ta Majalisar Dinkin Duniya,MDD, UNICEF Henrietta Fore ta bayyana wannan matakin a matsayin abu mai sosa rai, tace yawancin wadannan yaran da ake rabawa da iyayensu ‘yan kanan ne da basu mallaki hankalinsu ba, amma an rabasu da iyayensu dake neman mafaka a nan Amurka.
Da yake magana a madadinta akan wannan lamarin mai magana da yawun hukumar ta UNICEF Christopher Boulierac ya ce ta kowace irin hanya yaran suka samu kansu cikin Amurka, yaro ai yaro ne kuma suna da yancin su samu kariya duk inda suke, kuma su kasance tare da iyayensu
Tsare mutum tare da raba shi da iyalansa abu ne dake tura mutun cikin halin kunci da damuwa wanda kuma hakan na iya tura yaran su zama fandararru, ko kuma su zamanto an bude kafar cutar dasu tare da sasu su kasance cikin yanayin damuwa a kowane lokaci, wanda bincike ya nuna cewahakan zai iya tasiri a rayuwarsu.
A lokacin da yake wa taron kananan ‘yan kasuwa jawabi jiya a nan Washington Shugaba Trump ya ci gaba da dagewa akan wannan matakin da ya dauka duk ko da shan suka amma yayi kemadagas ko a jikin sa, game da wannan sabon tsarin da gwamnatin sa ta bullo dashi na raba yara kanana da iyayen su a bakin iyakar dake kudancin Mexico domin kawai sun shigo ta barauniyar hanya.
Facebook Forum