Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Kamen Wadanda Ake Zargi Da Taimakawa Ta’addanci a Najeriya


Hedikwatar Hukumar Tsaron Farin Kaya Ta Najeriya DSS.
Hedikwatar Hukumar Tsaron Farin Kaya Ta Najeriya DSS.

Hukumomin tsaron Najeriya na ci gaba da kamen mutanen da ake zargi da taimakawa ta’addanci a kasar, baya ga 'yan kasuwar canji da ke tsare a hannunsu tun kusan watai 3 da suka gabata.

Kamen da jami’an tsaro ke yi a yanzu dai ya tabo sassan Najeriya da dama da suka kunshi jihohin Legas da Kaduna da Kano da Adamawa da kuma babban birnin tarayya Abuja da dai sauran su, kama daga ‘yan kasuwa, ‘yan canji da masu hakar ma’adanai.

Masu sharhi kan lamurran yau da kullum dai sun ce za’a iya kallon sabon salon kamen a mastsayin yunkurin dakile harkokin ta’addanci a Najeriya.

Kwararre kan harkar tsaro, Air Commodore Tijjani Gamawa mai ritaya, ya yaba da lamarin yana mai cewa, abin da ya kamata jami’an tsaro su yi kenan tuntuni.

Lauyan wasu daga cikin ‘yan canjin da aka kama, Barista Rulwanu Idris, ya ce ya zuwa yanzu ba su san halin da ake ciki ba kan wadanda aka kama da yake wakilta a kotu.

Daya daga cikin shugabanni a kungiyar ‘yan canji Alhaji Ibrahim Hala Hassan, ya shaida cewa suna goyon bayan gwamnati a yaki da ta’adanci, amma dai a yi bisa adalci.

Mutane sama 400 ne ke hannun hukumar tsaro ta DIA da ke tattara bayanan sirri kan lamurran tsaro, duk da dai babu wani cikakken bayani dangane da laifin da suka aikata ya zuwa yanzu.

Domin karin bayani saurari rahotan Halima Abdurra’uf.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG