A cikin wasikar da kungiyar yan’ canjin ta rubutawa Hukumar tsaro ta DSS, ta ce tun a ranakun 9, 10, 12 da kuma 16 ga wannan wata ta Maris ne hukumar ta gayyaci mambobinta 26 daga jihohi biyar dake fadin kasar don amsa tamboyi.
To sai dai kungiyar ta ce bayan amsa gayyatar jami'an tsaron, ba’a sake jin duriyarsu ba, haka kuma babu wani daga cikin iyalansu da aka baiwa damar ganawa dasu, duk da korafin da wasu daga cikin iyalen suka yi.
Kungiyar ta bayyana cewa daga cikin wadanda ke tsare din akwai masu fama da matsalar jinya da ke bukatar kulawa akan lokaci wanda hakan wata babbar barazana ce ga lafiyarsu.
Ta kara da cewa an ci zarafin mambobinta tare da take hakkinsu wajen ci gaba da tsare su ba tare da bayyana laifin da suka aikata ba balle a gurfanar da su a gaban kotu, la’akari da sashi na 35 na kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 kamar yadda aka yi masa gyarar fuska.
Sakataren gamayyar Kungiyoyin Arewa a Najeriya Abdulaziz Sulaiman, ya ce ya kamata a bi matakai da doka ta tanada don bincike saboda gudun take hakkin dan Adam.
Duk da damar da doka ta baiwa wasu hukumomin tsaro a Najeriya na gudanar da bincike kan wasu laifufuka da ake zargin wani mutum, hukuma ko kungiya da aikatawa, dokar ta bayyana hanyoyi da matakai da za’a bi wajen gudanar da binciken da zimmar gano bakin zare.
Ga rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim daga Abuja Najeriya.