Bayanai na nunin bikin magaji ya hana na magajiya a ‘yan shekarun baya-bayan nan a nan Nijar inda hukumomin kasar suka fi bai wa sha’anin tsaro fifiko a maimakon ayyukan inganta rayuwar jama’a a sakamakon yawaitar ayyukan ta’addanci. Lamarin da ya matukar haddasa kuncin rayuwa a karkara inda talauci da jahilici da rashin ingantaccen tsarin kiwon lafiya yafi shafar mata.
Mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed wacce ta ganewa idanuwanta zahirin halin da ake ciki a yankunan Maradi da Yamai ta sha alwashin fahimtar da Majalisar Dinkin Duniya bukatar tallafawa rundunar G5 Sahel don ganin an sassauta wahalhalun gwamnatocin da matsalar ta’addanci ta hanawa sakat.
A take wannan yunkuri ya samu goyon baya daga shugabar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Margot Elizabeth Wallstrom, mai mukamin ministar harkokin wajen Sweden wacce ta ce ita ganau ce a game da halin da mata ke ciki a Nijar saboda haka dole ne kasashen duniya su yi wani abu akan matsalolin da ta’addanci ya haddasa akan iyakokin kasahen Sahel. Tana mai cewa, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen isar da wannan sako a gaban kwamitin sulhu.
Ministar ayyukan ci gaban matan Nijar, Madame Elbak Hajiya Zeinabou Tari Bako ta yi murna da jin wannan labari.
Sai dai matemakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta ce ba girin-girm ba ta yi mai. Inda ta ce, yawanci a kasashenmu na Afirka idan aka kawo kudi ‘yan karkara ba sa gani saboda haka za su kokarin ‘ganin kowa ya gani ya kuma samu.’
Facebook Forum