Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Sudan ta Kudu Sun Sake Cimma Wata Yarjejeniya


 Riek Machar madugun 'yan tawaye wanda yanzu zai koma kan tsohon mukaminsa na mataimakin shugaban kasa a wata sabuwar yarjejeniyar da suka kulla a Uganda
Riek Machar madugun 'yan tawaye wanda yanzu zai koma kan tsohon mukaminsa na mataimakin shugaban kasa a wata sabuwar yarjejeniyar da suka kulla a Uganda

A karkashin sabuwar yarjejeniyar da suka kulla madugun 'yan tawaye zai koma kan mukaminsa na mataimakin shugaban kasa kana a kwao karshen yakin da suka kwashe shekara biyar suna yi

Shugabanin bangarorin kasar Sudan ta Kudu sun cimma yarjejeniyar samun zaman lafiya data tanadin sake maida shugaban yan tawaye Reik Macha bisa mukaminsa na mataimakin shugaban kasa da kuma yiwuwar kawo karshen yakin basasar shekaru biyar a kasar.

Ministan harkokin wajen Sudan Al- Diedry Ahmed shine ya bada wannan sanarwar a karshen shawarwarin da aka yi a kasar Uganda wadda shugabanin Ugandan Yoweri Museveni da takwaran aikinsa na Sudan Omar Al Bashi suka shiga tsakani.

Yarjejeniyar ta tanadi nada mataimakan shugaban kasa guda hudu ciki harda mace daga bangaren masu hamaiya.

An kula yarjejeniyar ce da nufin kawo karshen yakin daya barke a shekara ta dubu biyu da goma sha uku, bayan da aka bata tsakani shugaba Salva Kr da mataimakinsa a wancan lokacin shugaban yan tawaye Reik Machar.

Yarjejeniyar makamancin wannan da aka kula a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar ta wargaje shekara guda bayan an kula ta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG