Jakadan Nigeria a Saudiyya Isa Dodo ya nesanta kansa da zargin cewa yana da hannu wajen kai mata da sauran mutane Saudiyya don aiyukan hidima inda su kan kare cikin wahala da nadama.
Isa Dodo wanda a ka zanta da shi daga Riyadh, na maida martani ne ga labarin da wani dandalin yanar gizo SECRET REPORTERS ya yada da nuna jakadan na da hannu a wannan lamari da ya yi kama da fataucin bil adama.
Dodo ya ce kullum shi da jami'an sa na kara kaimi don bin kadun 'yan Nigeria da su ka samu matsala, idan ma su na hannun 'yan sanda ko gidan yari ne.
Ga alhazan da za su fara shiga Saudiyya a watan nan, Dodo ya ce su lura da tashin farashi kaya har ma da abinci don haka su yi tsimi da tanadi.
Kwanakin baya an samu mata mazauna Saudiyya da ke kokawa kan jefa su cikin ukuba da a ke yi a Saudiyya.
Wani direba da ya nemi tafiya bai samu ba don wata jinya da ya ke da ita, matar sa ta samu tafiya shekaru biyu shiru ta ki dawowa don ma har ta turo an saya ma ta gida a nan Najeriya ta bar mijin na sallallami.
Wasu kungiyoyin Islama da a ka zarga da hannu a wannan jigila sun yi watsi da zargin da hakan ya sanya kamfanonin kai mutane Saudiyya su ka fito karara su ka ce su ke wannan aiki kuma su na da rejista da duk hukumomin da su ka dace.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Facebook Forum