Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yiwa Halittar Bil' Adam Kwaskwarima


A karo na biyu an yi amfani da fasahar zamani wajan yiwa halittar dan Adam, kwaskwarima wace aka gudanar a jami’ar California, dake kasar Amurka. Daga dukan alamu babu alamar wata matsala da ka iya biyo bayan aikin da aka gudanar a kan mutumin na biyu.

Kimanin watanni uku kenan da suka wuce aka gudanar da irin aikin, akan mutun na farko a duniya, da aka aiwatar da kwaskwarimar tsarin hallita a jikin shi. Tsarin kwaskwarimar hallita na da matakai masu hadari.

Ana sauya jinin mutun don gujema wata cuta da mutun ke da ita ko ya gada daga zuriyar da ya fito, a watan Nuwambar 2017, aka gudanar da aikin akan Mr. Brian Madeux, mai shekaru 44, inda aka canza mishi tsarin halittar shi.

Wanda yake dauke da wata cuta da ake kira ‘Hunter syndrome’ cutace da take cikin bargon mutun, anyi amfani da na’urorin zamani wajen fitar da jini daga bargon jikin shi, batare da wata matsala da ta saka rayuwar shi cikin hatsari ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG