Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutun-mutumi Na Iya Aikin Da Mutun Mai Jini Ba Zai Iya ba


Daga yankan ciyawa, aikatau, har ya zuwa aikin otel da asibiti, har ma da rainon yara da kula da tsofaffi, mutun-mutumi na iya yin duk abin da mutane ke yi, tun ba yanzu ba. Waddanan na'urori na iya yin abubuwan da mutane ba za su iya yi ba.

Robot, zai iya aiki har na awoyi 24 a rana, batare da yaji gajiyaba, ko kasala. A koda yaushe ya kan tarbi mutane da murmushi, a cewar Simon Wang, na kamfanin kirkirar mutunmutumi na 'Canny Unisboro Technology' a Beijing.

Ya ce na'urorin za su iya aiki ba tare da sun gaji ba, don hakan yasa daukar su aiki ya fi sauki maimakon daukar mutane masu aiki da jini aiki.

Misali, zai iya nuna ma mutun kasuwa, otel, gidan cin abinci da ma wasu wuraren, a cewar Wang, akwai wani mutun-mutumin da ake kira UU wanda yanzu haka ya fara aiki a China, a asibitoci domin gano lafiyar mutane ko rashin lafiyar da ke damun mutun, har da amsa wasu tamboyin da suka shafi kiwon lafiya.

Bugu da kari mutun-mutumi na iya ayuka masu wuya, kuma suna aiki a yanayi masu hadari da ban tsoro da idan mutun aka sa zai ji dari-darin aiki a wajajen ko dan tsoro.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG