Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan Boko Haram Sun Datse Hanyoyin da Suka Shiga Baga Kafin Su Kai Hari


Barnar da aka yi a garin Baga
Barnar da aka yi a garin Baga

Kungiyar Boko Haram ta kama Baga biyo bayan dirar mikiya da ta yiwa wannan garin na masuhunta.

Wani ganao da ya tallake rijiya da baya yace maharan sun shiga garin ne cikin motoci da babura.

Da suka shiga garin sai wasu daga cikinsu suka soma jefa nakiyoyi tare da cinnawa gine-gine wuta. Bayan hakan sai aka goce da kazamin fada tsakaninsu mayakan da sojojin Najeriya dake garin.

Wani jami'in leken asiri a Maiduguri yace sojojin Najeriya sun ja daga da 'yan Boko Haram. Amma yace ba tare da kaiwa sojojin wani doki ba da wuya sojojin dake ciki su iya rike garin.

Mayakan sun toshe hanyoyin shiga da fita daga garin. Mazauna garin sun tsere cikin dazuka wasu kuma suka nufi tafkin Chadi suka shiga kwale-kwale suka yi kokarin nunkaya domin su tsira. Wasu kuma ruwa ya cisu sakamakon haka. Wasu an harbesu har lahira. Wasu kuma sun jikata.

Har yanzu ba'a san adadin wadanda suka mutu ko suka jikata ba. Wani masunci da ya tsira ya gayawa Muryar Amurka cewa wasu sojojn sun tube kayan aiki suna rokon a basu fararen kaya sabili da albarusansu sun kare.

Garin Baga yana karkashin mazabar dan majalisar dattijai Maina Ma'aji Lawal a jihar Bornon. Karewa dai sanatan dan garin Baga ne. Yace mayakan sun dira kan garin wajejen karfe shida na safe zuwa karfe tara na safen sun gama da garin.

Sanata Lawal yace hukumomi a yankin da kuma matakin jiha sun gayawa rundunar sojojin Najeriya cewa ga fa irin barazanar da kungiyar Boko Haram ta ke yiwa yankin. An gaya masu inda suke kuma an gabatar da rahoto. Sanata Lawal yace bai san yadda zai yi bayanin yadda Baga ya fadi a saukake ba. Lamarin abun takaici ne-inji Sanata Lawal.

An san kungiyar Boko Haram da kai farmaki akan sansanonin sojoji saboda su samu karin makamai da zasu sa su kara karfinsu. Garin yana kan gabar ruwan tafkin Chadi ne wanda ya ratsa kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi. An kafa sansanin sojojin ne a matsayin wurin hadin gwiwar sojojin kasashen da zummar yaki da masu fasakwari da ta'adanci.

Akwai alamun cewa sojojin Najeriya ne kadai suke sansanin lokacin da aka kai harin. Masu fashin baki akan harkokin tsaro sun gayawa Muryar Amurka cewa kama garin Baga ya sabunta irin damuwa da ake nunawa kan kwarin gwiwa da karfin damarar sojojin Najeriya. Sojoji da suke aiku a arewa maso gabas sun yi kukan cewa basu da wadatattun kayan aiki har da albarusai domin tunkarar 'yan yakin sa kan.

Kafofin yada labaran Najeriya sun bada rahotannin cewa kotun soja ta ya yankewa wasu sojoji hukuncin kisa saboda bori da suka yi da kuma kin tafiya faggen yaki. Akwai wasu kuma masu yawa da aka ce suna dakun hukunci.

XS
SM
MD
LG