Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Nijar Ta Karbi Alluran Riga-kafin COVID-19 Karkashin Shirin COVAX


COVAX Nijar
COVAX Nijar

A Jamhuriyar Nijar, hukumomin kasar sun karbi wani tallafin allurar riga-kafin COVID 19 a matsayin wani bangare na gudunmawar da manyan kasashen duniya suka yi alkawarin bayarwa a karkashin tsarin COVAX da nufin yakar annobar a duk fadin duniya.

Allurai kimanin 355,000 na kamfanin AstraZeneca ne wasu manyan kungiyoyin duniya da suka hada da GAVI, UNICEF, OMS, EU da Bankin Duniya da kasashe aminai irinsu Amurka suka damkawa hukumomin kasar Nijar.

Jakadan Amurka Eric Whitaker, yayin bikin bada wadanan magunguna ya ce, Amurka na daga cikin kasashen da suka yi na’am da bukatar tallafawa kasashe kimanin 92 da ingantaciyar allurar riga-kafin wannan cuta a karkashin tsarin COVAX.

Amb. Eric Whitaker Jakadan Amurka a Jamhuriyar Nijar
Amb. Eric Whitaker Jakadan Amurka a Jamhuriyar Nijar

A cewar shi, hakan ya sa kasar ta bada gudunmawar biliyan 2 na Dalar a wannan tafiya da duniya ta sa gaba.

Da yake karbar wannan tallafi, Fira Minista Ouhoumoudou Mahamadou, ya yaba da wannan yunkuri da ya kira hanyar samar da walwala ga talakawa.

A karshen watan jiya ne aka kaddamar da kamfen na riga-kafin cutar Coronavirus a birnin Yamai sakamakon wani tallafin da kasar China ta baiwa Jamhuriyar Nija.

Hakan ya sa hukumomi yanke shawarar aika wannan tallafi na tsarin COVAX zuwa sauran yankuna in ji Ministan kiwon lafiya Dr. Iliassou Idi Mainassara.

A tsakiyar watan Maris na 2020 ne aka gano mutun na farko da ya kamu da cutar a Nijar lamarin da ya sa kasar daukan matakan kariya da nufin dakile yaduwar wannan masifa.

Amma da yake ance riga-kafi ya fi magani, ya sa kasar a sahun kasashen da suka yi na’am da allurar riga-kafi.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Jamhuriyar Nijar Ta Karbi Alluran Riga-kafin COVID-19 Karkashin Shirin COVAX
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG