Jami'an yan sanda guda biyar basu amsa laifin caje cajen cewa sun kashe shugaban kungiyar Boko Haramun ne, shekaru biyu da suka shige ba.
Talata aka caji jami'an yan sanda gaban wata kotu a Abuja, baban birnin taraiyar Nigeria da laifin cewa ba bisa ka'idar doka ba, suka kashe Mohammed Yusuf da wasu magoya bayansa da laifin aikata tarzoma.
Mohammed Yusuf shine shugaban kungiyar Boko Haramun ne, wadda ta tada kayar baya a galibin jihohin arewacin Najeriya a shekara ta dubu da tara, da suka sa ala tilas aka yi amfani da sojoji wajen kawo karshensa. An kashe fiyeda mutane dari takwas a rikicin, ciki harda shi Mallam Yusuf.
Kungiyar ta dade tana zargin cewa Mallam Yusuf ya mutu ne a lokacinda yake tsare a hannun ‘Yan sanda.
Ita dai kungiyar Boko Haramun ne tana so a kaddamar da amfani da shari'ar Musulunci a jihohin arewacin Nigeria, bata mutunta tsarin mulki da gwamnatin taraiyar Nigeria.
Ana dorawa kungiyar laifin munanan hare haren bama bamai da kwantar bauna da suka hadasa kaurar mutane daga Maiduguri, jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria a farkon wannan wata.
Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria yayi tayin zantawa da yan kungiyar da nufin kawo karshen tarzomar. To amma shugabanin kungiyar sunce ba zasu gana da jami'an tsaron da suke kokarin ragargaza su ba
Wasu jami'an yan sandan Nigeria guda biyar basu amsa laifin kashe shugaban kungiyar Boko Haramun ne
Wasu jami'an yan sanda Nigeria guda biyar, basu amsa caje cajen sun kashe shugaban kungiyar Boko Haramun ne shekaru biyu da suka shige ba. Talatan nan aka caji yan sandan a wata kotu a Abuja, baban birnin taraiyar Nigeria.