Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu nazarce nazarce da aka yi sun nuna cewa maganin jinyar kanjamau, suna kuma yin rigakafi


Maganin rigakafin kanjamau ko SIDA.
Maganin rigakafin kanjamau ko SIDA.

Wasu nazarce nazarce da aka yi da aka gabatar da sakamakon Laraban nan sun nuna cewa, magungunan da ake amfani dasu wajen jinyar kanjamau, suna iya yin rigakafin harbuwa da kwayar cutar ta kanjamau ko SIDA.

Wasu nazarce nazarce biyu da aka yi sun nuna cewa magungunan da aka kirkiro domin jinya ko kuma rage kaifin kwayar cutar kanjamau ta HIV za su kuma iya yiwa mutane rigakafin harbuwa da kwayar cutar dake haddasa kanjamau ko SIDA.

Sakamakon binciken da aka gudunar bisa jagorancin Amurka wanda aka gabatar da sakamakonsu a jiya Laraba, sun nuna cewa shan magungunan rage tsananin cutar kanjamau a kullu yaumin na rage kasadar mutum ta kamuwa da cutar tsakanin mace da miji.Dukkannin binciken biyu dai a Afirka aka gudanar, inda anan ne aka fi samin wadanda suka harbu da kwayar cutar HIV a duniya.

Cibiyar Bincike da kayade yaduwar Cututtuka ta Amurka da ake cewa CDC a takaice wadda cibiyarta ke birnin Atlanta jihar Georgia, itace ta gudanar da daya daga cikin gwaje-gwajen da aka yi, inda aka yi amfani da wadanda basu harbu da kwayar cutar ba, su dubu daya da maitan, maza da mata a kasar Botswana. An baiwa kusan rabin wadannan mutane magungunan jinyar kanjamau, daya rabin kuma aka basu maganin giri da ake cewa placebo.

Binciken ko kuma gwaje gwajen sun nuna cewa wadanda aka baiwa maganin jinyar kanjamau, ya rage musu kasadar kamuwa da cutar da wajen kashi saba';in da takwas daga cikin dari.

Asusun Bill da Melinda Gate shine ya bayar da kudin gwaji na biyu karkashin jagorancin jam'iyar Washington. Wannan gwajin ya kunshi maza da mata dubu hudu da dari bakwai a kasashen Kenya da Uganda. Rabin mutane sun harbu da kwayar cutar dake hadasa kanjamau, rai kuma basu harbu da kwayar cutar ba

Abinda aka yi sai aka rinka baiwa wadanda basu harbu da kwayar cutar ba, maganin giri ko kuma wasu irin magungunan jinya. Sakamakon binciken ya nuna cewa an samu ragowar harbuwa da kwayar cutar kanjamau da wajen kashi sittin da uku zuwa kashi saba'in da uku daga cikin dari

Wannan sakamako ya daddawa direktan cibiyar CDC. Dama kuwa gwaje gwaje ko kuma nazarce nazarcen da aka yi a baya sun nuna ragowar kamuwa da kanjamau tsakanin maza masu luwadi. To amma sakamakon wannan bincike sune na farko da suka nuna cewa shan magungunan jinyar kanjamau suna da kaifin bada kariyar harbuwa da kwayar cutar dake hadasa kanjamau...

XS
SM
MD
LG