Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya gabatar da shawarar cewa, a yiwa tsarin mulkin Nigeria gyara da zai kayyade wa’adin mulki shugaba dana gwamnoni zuwa wa’adi daya kurum, amma kuma mai dan tsawo.
A jiya talata shugaba Jonathan ya bada sanarwar wannan shiri, a yayinda yake fatar yin haka zai baiwa yan siyasa damar maida hankali wajen yiwa jama’an da suka zabe su aiki, maimakon maida hankali akan kokarin ganin an sake zabensu. Haka kuma shugaban yace daukan wannan mataki zai sa ayi tsimin kudin da ake kashewa wajen gudanar da zabe.
Sanarwar tasa bata fadi takamame yawan shekaru da za’a kayyade a wadi da zasu yi. Yanzu dai wa’adin mulkin shekaru hudu hudu ne aka amfani dashi, kuma sau biyu mutum zai iya tsayawa takara.
Haka kuma ya bada shawarar suma wakilan Majalisu a kara yawan shekarun wa’adinsu, amma, su suna iya neman a sake zabensu.
A cewarsa idan aka amince da wannan shawara, to ba za’a fara amfani da shirin ba, a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, a lokacin ya kamalla wa’adin mulkinsa na yanzu.