Rahoton binciken da mahukuntan sojojin Amurka suka fitar akan sanadiyar kashe wasu sojojinta hudu a Jamhuriyar Nijar tare dana Nijar su hudu a watan Oktoban bara, ya nuna cewa sojojin na Amurka basu samu izinin kai farmakin da suka kai ba.
Rahoton mai shafi takawas ya nuna babu wani dalili da zai sa sojojin su kai farmakin har ma a yi masu kwantan bauna ranar 4 ga watan Oktoban shekarar 2017 a kusa da kauyen Tongotongo dake da tazarar kilomita 200 daga Yamai babban Birnin Nijar.
Rahoton ya gano wasu kura kurai da suka hada da cewa sojojin Amurka 12 dake kasar basu samu wani umurni daga shugabanin su. A saboda haka babu wani dalilin bin sojojin Nijar wajen farautar wani dan gwagwarmayar Islama na kungiyar ISIS a yankin.
Rahoton ya yi bayani akan yadda lamura suka tabarbarewa sojojin Amurka da na Nijar yayinda suka tsaya a kauyen Tongotongo inda suka fuskanci barazanar harbe harbe.
A cewar masu binciken ‘yan bindiga kusan guda dari ne suka kaiwa sojojin Amurka da na Nijar hari. Duk da cewa sun sanar da sansaninsu halin da suka samu kansu ciki, basu nemi taimakon gaggawa ba.
Sojojin Amurka da suka rasa rayukansu a cikin wannan artabun sun hada da Saje David Johnson, da Uztaz Ibrahim Blake, da Jeremiah Dowson da kuma Justin Wright.
Bayan kimanin mintoci 50 ne dakarun Faransa suka isa wurin domin taimakawa sojojin Amurka, inda suka fuskanci ‘yan ta’adan.
Ga karin bayani daga fasarar da Abdulaziz Adili Toro ya yi
Facebook Forum