Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Rundunar Sojin Sama Ya Hallaka Fiye Da ‘Yan Ta’adda 28 A Jihar Neja


Jirgin yakin Najeriya (Twitter/Nigerian Airforce)
Jirgin yakin Najeriya (Twitter/Nigerian Airforce)

Harin da rundunar sojin saman Najeriya ta kai a karamar hukumar Shiroron jihar Neja ya hallaka fiye da ‘yan ta’adda 28.

Harin da rundunar sojin saman Najeriya ta kai a karamar hukumar Shiroron jihar Neja ya hallaka fiye da ‘yan ta’adda 28.

Mukaddashin Darakatan Yada Labaran Rundunar, Group Kyaftin Kabiru Ali, ne ya bayyana hakan a sanarwar daya fitar a yau Alhamis.

Ya kara da cewa, sashen mayakan sama na aikin wanzar da zaman lafiya mai taken “Operation Whirl Punch” ne ya kai harin a jiya Laraba, 11 ga watan Satumbar da muke ciki.

“Hare-haren sun yi mummunan tasiri, inda suka hallaka dimbin ‘yan ta’adda nan take. A yayin hada wannan rahoto, an kwashe gawawwaki 28 daga yankin, sannan ana cigaba da tattaro karin wasu ‘yan ta’addar da makamai da konannun babura daga yankin.”

Rundunar sojin saman ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cigaba da kai hare-hare ta sama akan kanta ko ta hanyar yin hadin gwiwa da sojin kasa, domin kawar da barazana ga zaman lafiya da bunkasar arziki da tsaron gagarumar kasarmuNajeriya.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG