Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yanka Ta Tashi A jihar Gombe


Lawyers in the court
Lawyers in the court

Wannan rigimar dai ta samo asali ne tun daga zaben fidda gwani na jamiyyar APC a jihar Gombe, game da wanda zaiyi takarar wakiltan Funakaye, kwami da Gombe a majilisar tarayyar Najeriya.

Bayan Kammala zaben ne na fidda gwanin ne aka bayyana Yaya Bauci a matsayin wanda yayi nasara wanda ya samu kuriu dari shidda da goma sha biyu,(612).

Yayin da Hamisu Mai lantarki ya samu dari da casein(190), sai kuma Dr Umar ya samu kuriu goma kacal(10).

Wannan ne yasa Yaya Bauci ya shiga babban zaben inda ya samu nasara akan sauran jamiyyu, al’amarin da baiyi wa Honarabul Hamisu Mai Lantarki dadi ba, wanda hakan yasa ya garzayo nan Abuja inda ya samu hukncin wata kotu wanda yasa hukumar zabe ta ayyna shi a matsayin wanda zai karbi takardan shaida.

Shima wannan hukuncin baiyi wa Yaya Bauci dadi ba, inda shima ya shigar da kara a wata kotun na daban.

Ko da yake bai samu nasara ba al’amarin da yasa ya daukaka kara a kotun daukaka dake nan Abuja.

A hukuncin data yanke ta jingine hunkuncin farko da karamar kotun ta zartas da tasa ta baiwa Hamisu mai lantarki takardan shaida.

Ga Hassan Maina Kaina da ci gaban rahoton 2’12'’

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG