Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Tara Haraji Ta Amurka Tana Bin Coca-Cola Haraji Fiyeda Bilyan Uku


Kamfanin Coca-Cola
Kamfanin Coca-Cola

Kamfanin sarrafa lemun kwalba Coca-Cola ya kalubalanci.

Kamfanin sarrafa lemun kwalba, Coca-Cola ya ce ya sami takarda daga hukumar haraji ta Amurka da ake kira IRS a takaice ko cikakkiyar sunanta Internal Revenue Service, cewa ana binsa harajin dala milyan dubu uku da milyan dari uku.

A bayanan da kamfanin ya bayar a kasidu da ya shigar ta hanun hukumar kula da hannayen jari a jiya jumma'a, Cola Cola yace zai kalubalanci wannan magudan kudi da hukumar ta ayyana.

Kamfanin Coca Cola yace takaddamar ta samo asali ne daga yadda yake amfani da bayanai kan lasisin sarrafa lemun kwalba a kasashen waje, da kuma sayarwa.
kamfanin sarrafa lemun kwalban yace yana bin tsarin da hukumar harajin ta shimfida a 1996.

kamfanin yace IRS bata wani gargadi gameda wannan mataki kafin ta dauke shi ba. Kuma tuni hukumar ta sanarwa Coca Cola cewa tana nazarin daukar matakin shari'a domin amsar wadannan kudade.

Coca Cola ya hakikance cewa harajin da hukumar take ikirari bashi da tushe kuma zai dauki duk mataki a hukumance data fuskar shari'a wajen warware wanan takaddama.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG