Kwanakin baya ne shugaba Muhammad Buhari ya bayyana kudurin gwamnatinsa na daukan sabbin 'yansanda dubu goma. Tun daga lokacin ake jira a ji yadda za'a zakulo sabbin 'yansandan.
Mataimakin babban sifeton 'yansandan DIG Hashimu Argungu ya bayyana tsarin da zasu bi su samo sabbin 'yansanda dubu goman da ba bata gari ba ne.
Yace na daya zasu bi inganci. Zasu fara daukan sabbin 'yansandan daga kananan hukumomi. Yace a kowace karamar hukuma akwai shugabanta sannan akwai sarakuna da malaman addini da babban dansandan yakin ko DPO. Wadannan ne zasu ba duk wanda za'a dauka takardar amincewarsu cewa dan asalin wurin ne kuma yana da dabi'u da halaye nagari.
Band shugabannin rundunar zata yi aiki da kungiyoyin al'umma su sa ido. Idan sun ga an sa wani dake da mugun hali su gayawa rundunar wadda zata bincika ta tabbatar ba'a dauki wani bata gari aiki ba.
DIG Hashimu Argungu yace idan an kawo dansanda mai kishin kasa ba mai son handama da babakere ba da cin amana da nuna banbanci ba to za'a samu 'yansanda nagari.
Tsohon ministan 'yansandan Najeriya Alhaji Adamu Maina Waziri yace adadinsu yayi kadan ainun. Yace akwai gibi na 'yansanda na akalla miliyan uku da dubu dari bakwai idan aka yi la'akari da adadin al'ummar kasar miliyan dari da sittin. Idan an bi misalin kasashen da suka cigaba ana neman 'yansanda miliyan hudu.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.