To amma tambayarta shine, menene ingancin shaidar auren in har ba sa hannunta a matsayin jami’ar da ke kula da wannan bangaren.
Jim kadan bayan Kim Davis ta shiga ofishinta, sai mataimakinta Brian Mason ya dankawa matan Shannon Wampler da Carmen Collins da suka auri junansu takardar shaida.
Davis ta koma aiki bayan ta yi kwanaki 5 a kulle bisa bijirewa dokar gwamnatin tarayya ta Amurka da ta halarta auren jinsi daya tun a watan Mayun da ya wuce.
Ta ki sa hannu a takardar shaidar irin wannan aure bisa cewa, addininta bai bata damar yin haka ba.
Kim dai tace auren jinsi daya ya sabawa darikarta ta Apostolic a cikin addinin Kirista da take bi. Ta kuma zama jarumar wasu masu ra’ayin Kiristanci tsantsa a Amurka.
Amma ita Davis tace ba jaruntaka bane, sannan bata son ta zama abin cece ku ce akan maganar.
Mataimakinta Brian ya bada shaidar auren wasu maza ha sau bakwai da suka auri junansu a cikin mako daya da Kim take kulle.
Tace ba zata hana mataimakin ya bayar ba, amma menene ingancin shaidar da bata da sa hannunta?
Gwamnan Kentucky da babban Lauyan jihar sun tabbatar da ingancin takardun shaidar auren da mataimakin nata ya bayar cewa suna da inganci kuma bisa doka.