Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Gwamna Yace Da Sauran Rina A kaba


Court Nigeria
Court Nigeria

Duk da yake dai kotun sauraren kararrakin zabe tayi watsi da karar da tsohon gwamnan jihar Zamfara Alhaji Aliyu Mamuda Shinkafi suka shigar shi da jamiyyar sa ta PDP .

Inda suke kalubalantar zaben Alhaji Abubakar Abdul Azeez Yari na jamiyyar APC a matsayin gwamnan jihar a waadin mulki na biyu.

Tsohon gwamnan yace sam basu gamsu da hukuncin na kotun ba, inda yasha alwashin ci gaba da daukaka karar zuwa kotun koli.

Mamud Shinkafi shima wanda yayi takara gwamnan a waadin mulkin san a biyu, yace yayi mamaki da hukuncin da kotun ta yanke duk ko da dinbin hujjojin da aka gabatar mata akan karar.

To sai dai da aka tambayi tsohon gwamnan ko me wannan matakin nasa ke nufi ga demokaradiyyar Najeriya?

‘’Ni ba don kaina nake yi ba sabo da al’umma ake yi kuma suna sa rai idan ka duba tun lokacin da ake wannan hukunci duk gari ba wanda yayi murna duk gari kamar anyi mutuwa ne, mun san talakkawa sun zabe mu aka zo akayi canje-canje sabo da haka zamu ci gaba mu karbo wa talakka hakkin sa har zuwa karshe’’.

Ga Murtala Faruk Sanyinna Da karinBayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG