Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shiga Fargaba Kan Takunkumin ECOWAS A Iyakar Nijar Da Najeriya


Taron Shugabannin Kungiyar ECOWAS kan juyin mulki da sojoji su ka yi a Nijar
Taron Shugabannin Kungiyar ECOWAS kan juyin mulki da sojoji su ka yi a Nijar

Yanzu haka hankulan jama'a sun rarrabu game da maganar kakkabawa Nijar takunkumi da kasashen ECOWAS suka yi akan iyakar Nijar da Najeriya a Birni N'Konni, inda wadansu ke ganin cewa abin zai yi tasiri, yayin da wasu ke cewa, ECOWAS na tauna tsakuwa ne domin baiwa aya tsoro.

Garin Birni N'Konni, shine babban gari a Jamhuriyar Nijar mafi kusa da wata kasa ta ECOWAS, kasancewa mita 500 ne kacal tsakanin Jami'an tsaron Nijar da takwarorin su na Najeriya a wannan iyakar ta Birni N'Konni a jahar Tahoua da karamar hukumar Illela ta tarrayar Najeriya.

Tun lokacin da taron shugabanin kasashen kungiyar ta ECOWAS na karshe a makon jiya da ya wakana a Abuja, shugabanin suka yanke shawarar kakabawa Jamhuriyar Nijar takunkumai tare da bai wa askarawan kasa da suka karbe mulki daga Mohamed Bazoum sati guda na mayar da shi kan kujerar sa, ra'ayoyi suka soma cin karo da juna game da tasiri ko akasin haka na kulle iyakokin kasashen ECOWAS da Nijar.

Mohamed Bazoum
Mohamed Bazoum

Wadansu yan Najeriya da ke kasuwancin kai komo a kan iyakar, sun ce, takunkumai na hana shiga da fita a Nijar, na iya shafuwar tattalin arzikin kasashen 2 da al'ummomin su.

Sai dai a cewar wani manazarcin al'amuran yau da kullum, barazanar takunkumin tauna tsakuwa ne kawai don aya ta ji tsoro, domin ba zai yi wani tasiri ba.

Yan kasuwar na Nijar da ke shiga Najeriya suna kawo abinci a Nijar, cewa suka yi takunkumi na iya jefa mutanen Nijar da ma na Najeriya da ke wannan yankin a cikin wata matsala.

Malam Maman Hassan masani tattalin arziki ne, ya kuma ce akwai matsalolin da ke iya bijirowa da zaran an saka wa Nijar takunkumi kamar yadda ECOWAS ta yi barazana.

Yanzu haka iyakokin na Nijer na kulle, yayin da jama'a suka zura idanu don ganin menene zai faru bayan wannan barazanar ta ECOWAS da hadakar kasashen yammacin nahiyar Africa.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:34 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG