Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako Faransawan Da Aka Sace Aka Kai Najeriya


'Yan'uwan Faransawan da aka sace a Kamaru aka kai Najeriya, su na magana da 'yan jarida a Paris, bayan da aka sako 'yan'uwansu, Jumma'a 19 Afrilu, 2013
'Yan'uwan Faransawan da aka sace a Kamaru aka kai Najeriya, su na magana da 'yan jarida a Paris, bayan da aka sako 'yan'uwansu, Jumma'a 19 Afrilu, 2013

Shugaba Francois Hollande yace an sako mutanen tare da taimakon Najeriya da kamaru, amma bai fadi yadda aka sako su ko aka kwato su ba.

An sako wasu Faransawan da aka sace daga yankin arewacin Kamaru, aka tafi da su Najeriya watanni biyun da suka shige.

Wakiliyar Muryar Amurka a Paris, Lisa Bryant, ta ce shugaba Francois Hollande na Faransa ya bayyana sako iyalan Moulin-Fournier a zaman wani babban abin kwantar da hankali, yana mai fadin cewa an samu sukunin sako su tare da taimakon Najeriya da Kamaru.

Mr. Hollande yace ya tattauna da maigidan wannan iyalin da ya kunshi mutane 7, kuma su na cikin koshin lafiya.

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, yana kan hanyarsa ta zuwa Yaounde domin ganawa da iyalin, wadanda zasu koma gida nan da 'yan kwanaki.

A farkon watan Fabrairu aka sace Faransawan su 7 a arewacin Kamaru, aka tsallaka da su cikin Najeriya. An yi imanin cewa 'yan kungiyar na ta Boko Haram ce suka sace su. A cikin wani faifan bidiyo da aka sanya a kan Intanet jim kadan a bayan sace su, 'yan bindiga sun yi barazanar hallaka su idan har ba a sako wasu 'yan'uwansu ba.

Shugaba Hollande da jami'an gwamnatin Kamaru ba su bayyana yadda aka yi aka sako mutanen ba, wadanda a cikin daren jiya alhamis aka mika su ga hukumomi.

A cikin wata hirara da aka yi da shi a gidan rediyon Faransa, ministan sadarwa na Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, bai ce ko an tattauna da tsageran da suka sace su ba, sai dai yace an samu hadin kai sosai a tsakanin Kamaru da Najeriya da kuma Faransa. A can baya, gwamnatin Faransa ta ce ba zata tattauna da masu garkuwa da mutanen ba.
XS
SM
MD
LG