Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Ce 'Yan Ta'addar Najeriya Sun Sace Faransawa A Kamaru


Wani jirgin saman yakin Faransa samfurin Mirage 2000 yana tashi daga filin jirgin saman Bamako a kasar Mali
Wani jirgin saman yakin Faransa samfurin Mirage 2000 yana tashi daga filin jirgin saman Bamako a kasar Mali

Shugaba Francois Hollande ya fadawa ‘yan jarida cewa yayi imanin ‘yan bindigar da suka sace Faransawan sun tsere da su zuwa cikin Najeriya.

An sace wasu Faransawa 7 ‘yan yawon bude ido da shakatawa, cikinsu har da yara 4, a kasar Kamaru, a wani lamarin da shugaba Francois Hollande na Faransa yace wasu ‘yan ta’adda ne daga Najeriya suka sace su.

A lokacin wani rangadin da ya kai kasar Girka jiya talata, Mr. Hollande ya fadawa ‘yan jarida cewa yayi imanin ‘yan bindigar da suka sace Faransawan sun tsere da su zuwa cikin Najeriya.

Shugaba Hollande ya ce, "Muna jin abinda ya faru shi ne an gudu da mutanen da aka sace din, aka tsallaka da su zuwa cikin Najeriya. Muna bakin kokarinmu wajen farauto ‘yan bindigar, amma muna gargadin ‘yan yawon shakatawa dake yankin na Kamaru da su guji yin abubuwan da zasu jefa su cikin irin wannan hatsarin. Zamu yi duk abinda zamu iya domin samo ‘yan kasarmu."

Faransawan su 7 da aka sace duk ‘yan gida daya ne. Kamfanin makamashi na Faransa mai suna GDF Suez yace an sace wani ma’aikacinsa tare da iyalinsa a lokacin da suke yin hutu a arewacin Kamaru.

Wannan lamarin ya faru ne kwana daya a bayan da wata kungiya mai suna Ansaru ta dauki alhakin sace wasu ‘yan kasashen waje su 7 a arewacin Najeriya.

An sace mutanen wadanda ke aiki ma wani kamfanin kasar Lebanon, a lokacin da ‘yan bindiga suka far ma inda suke aiki a garin Jama’are dake Jihar Bauchi.

Har ila yau, kungiyar ta Ansaru ta dauki alhakin sace wani Bafaranshe a watan Disamba.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG