Laurent Fabius yace an yi garkuwa da wani injiniya kuma dan kasar Faransa a Najeriya cikin watan Disamba.
Fabius ya yi hira da manema labarai bayan tattaunawarsu da shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan jiya asabar.
Ya bayyana cewa an ga mutanen bakwai ‘yan gida daya a wani hoton bidiyo da aka sa a yanar duniyar gizo ta Yutub a bakin gandun dajin kasar Kamaru dake lardin arewacin kasar wata guda da ya shige. Hukumomi suna kyautata zaton cewa, an sace iyalin ne a Kamaru aka tafi da su Najeriya
Ministan harkokin kasashen ketare na Najeriya Olugbenga Ashiru yace gwamnatin tarayyar Najeriya da dukan hukumomin tsaro suna yin iyaka kokari na ganin an saki mutanen da ake garkuwa da su lami lafiya.
Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin garkuwa da su. Kungiyar ta shiga kai kare hare a fadin Najeriya a matsayin maida martani da matakin da sojojin Faransa suka dauka a Mali.