Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Baza Muyi Musaya Da Boko Haram Ba - inji Faransa


Motocin yakin Faransa a Bamako akan hanyarsu ta zuwa garin Mopti.
Motocin yakin Faransa a Bamako akan hanyarsu ta zuwa garin Mopti.

Faransa tace ba zata yi shawarwari da mutanen da suka kama wasu ‘yan kasarta cikin makon jiya a Kamaru suna garkuwa da su ba.

WASHINGTON, D.C - Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ya fada yau talata cewa “Faransa zata yi amfani da duk wata dama” wajen ganin an sakar mata ‘yayanta, duk da haka yace ba zata yi shawarwari da nufin wata musaya ba.

Ministan yayi magana ne kwana daya bayanda wani fefen bidiyo da aka saka a dandalin Youtube ya nuna wasu ‘yan bindiga suna magana da larabci suna gargadin cewa zasu kashe rukunin wasu mutane da ake garkuwa dasu, muddin ba'a saki wasu mayakan sa kai masu ikirarin Musulunci da hukumomi suke tsare dasu a Najeriya da Kamaru ba.

Fefen bidiyon yana dauke ne da hoton maza biyu, mace daya da yara hudu wadanda ke zaune karkashin wata rumfa, tare da wasu mutane da suke rufe da fuskokinsu, kuma suna kewaye da su.

Daya daga cikin ‘yan Faransan da ake garkuwa dasu yace kungiyar Boko-Haram ta Najeriya ce take garkuwa da su.

Faransawan dai, su bakwai duk 'yan dangi daya ne, kuma an sace su ne a cikin makon jiya a Kamaru lokacin da suke hutu, kuma sai tayu an kai su makwabciyar kasa Najeriya.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG