Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

#ENDSARS: 'Yan Najeriya Na Shakkun Bayyana Gaban Kwamiti


Kotun Tarayya a Maitama, Abuja
Kotun Tarayya a Maitama, Abuja

‘Yan Najeriya da dama suna dari darin bayyana gaban kwamitin da gwamnati ta kafa da zai saurari kararrakin cin zarafin da ake zargin jami'an 'yan sandan SARS suka yi domin gudun kada a yi masu bita da kulli.

Makonni bayan bada umarnin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi na kafa kwamitocin bincike kuntatawa al’umma da jami’an ‘yan sandan SARS suka yi, daya daga cikin bukatun da matasan da suka gudanar da zanga zangar neman soke kungiyar suka gabatar, ‘yan Najeriya da dama suna dari darin bayyana gaban kwamitin domin gudun kar kilu ta jawo bau.

Binciken da Sashen Hausa ya gudanar na nuni da cewa, I zuwa yanzu ba a kafa kwamitocin a wadansu jihohi ba, yayinda a jihohin da aka kafa kwamitin, mutane da dama suna shakkun ribar da zasu yi idan suka bayyana gaban kwamitin, wadansu mutane sun bayyana cewa, suna iya sake fadawa cikin hadari ko ma su rasa rayukansu a hannun wadanda suka gasa masu akuba idan har suka kai kara gaban kwamitin da zai bukaci jami’an tsaron su bayyana domin sauraron korafin da kuma kare kansu.

IG Wala, Dan gwaggwarmaya a Najeriya
IG Wala, Dan gwaggwarmaya a Najeriya

A cikin Hira da Sashen Hausa dan gwaggwarmaya Ibrahim Garba Wala da aka fi sani da IG Wala, wanda ya jagoranci gangamin neman kawo karshen cin hanci da rashawa a Najeriya a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu ya ce yana daga cikin wadanda suke da wannan tunanin.

Sai dai wadansu sun rungumi wannan damar tare da bayyana a gaban kwamitin inda suka yi ido hudu da wadanda suka gasa masu akuba bayan shekaru da cin zarafinsu.

A zaman kwamitin da ake yi a babbar kotun tarayya dake Maitama, Abuja, da ya fara cikakken zama makon farko tun bayan kafa shi, wadanda suka bayyana a gaban kwamitin sun hada da wadanda jami’an SARS suka kashe danginsu, da wadanda suka yi amfani da karfin kaki suka kwace masu kaddarori, da wadanda aka kulle aka kuma gasawa akuba, da wadanda aka nakasa da harbin bindiga da dai sauran ayyukan cin zarafin bil’adama.

Chris Richard, mahaifin wata yarinya da 'yanda suka harba
Chris Richard, mahaifin wata yarinya da 'yanda suka harba

Christ Richards wani dan jarida wanda ya kware a fannin rubuta rahotannin aikata miyagun laifuka, ya sami kansa a cikin wannan yanayin inda jami’an SARS suka dirkawa ‘yarsu bindiga a baya har sau biyu suka nakasa ta. Ya bayyanawa Muryar Amurka yadda lamarin ya faru.

Yace “Wannan wani lamari ne da ya shafi wata dalibar makarantar sakandaren Wuse, wadda harsashen da aka yi harbin kan mai uwa da wabin da ‘yan sanda suka yi ya shafe ta. Yan sandan da suke harbe ta sun ce wai suna bin ‘yan Shi’a ne da ke kan hanyarsu daga wajen Bega za su shiga cikin gari inda zasu je su tada hankali. Yarinyar kuma tana fitowa daga unguwar Wuse a daidai wani gidan cin abinci da ake kira Greenplate, kusa da inda motocin sufuri ke daukar fasinja a Wuse, sai kawai taji an dirka mata harsashi a bayanta har sau biyu sai ta fadi.

endsars-yan-sanda-sun-zubawa-matashi-fetir-a-baya-suka-cinna-mashi-wuta-a-binuwe

ana-zargin-wani-dpo-da-azabtar-da-mutane-da-tabarya-a-bauchi

zanga-zangar-endsars-a-najeriya-ta-kawo-rarrabuwa-a-wasu-fannoni

Lauyan daya daga cikin wadanda suka bayyana gaban kwamitin wanda da karfi da yaji aka kwacewa fili ya bayyana cewa babu alamar za a yiwa mutumin adalci

Yace "wannan ya fusta wanda na ke karewa. Sabili da 'Dan sandan ya shantala karairayi, ba bu wani batu dake gaban kotu a halin yanzu, ya san cewa, menene zai sa su kwace fili da ake rigima a kai su rike takardun su kuma ce mutanen su je kotu?"

Banda masu gabatar da kara da lauyoyinsu da kuma wadanda ake kara, akwai kuma kungiyoyi masu zaman kansu da suke sa ido a zaman.

Deborah Yusuf, jami’ar wata kungiya mai zaman kanta da ake kira Dinin die Foundation, da ke hankoron kare hakkokin bil’adama ta tafi da kayan aiki na zamani domin nadar cikakken bayanan zaman. Ta bayyana cewa, "wadansu da ake karar basu bayyana gaban kwamitin, wannan kuma yana sa a dauki lokaci ba a kammala sauraron korafin mutum guda ba domin babu yadda za a iya wucewa zuwa wani dabam sai an ba mutanen da ake zargi da cin zarafi damar kare kansa."

Zaman kwamitin sauraron kararraki SARS a Maitama, Abuja
Zaman kwamitin sauraron kararraki SARS a Maitama, Abuja

Aikin kwamitin ya hada da gudanar da bincike kan sahihancin korafe korage da aka gabatar da nufin tabbatar da gaskiyarsu da kuma bada shawarar matakan da ya kamata a dauka, da suka hada da biyan wadanda aka cutar diyya, harda wadanda zanga zangar baya bayan nan ta shafa, da kuma neman hanyar shawo kan wannan matsalar nan gaba.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci kwamitocin su mika rahotonsu cikin watanni shida.

Kawo yanzu jihohi 26 da kuma babban birnin tarayyar Najeriya suka kafa kwamitocin, daga cikin jihohi 36.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti

#ENDSARS: 'Yan Najeriya Na Shakkun Bayyana Gaban Kwamiti-6:55"
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:55 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG