Rahotanni daga jihar Kaduna na bayyana cewa wasu dalibai 4 daga cikin daliban makarantar Bethel Baptist sun sami tserewa daga hannun ‘yan bindigar da suka sace su.
Wannan na zuwa ne kwan 4 bayan da ‘yan bindigar suka sako daliban makarantar 28 daga cikin 121 da suka yi awon gaba da su.
To sai dai a yayin da dalibai 3 da suka tsero daga ‘yan bindigar suka sami isa gida, na hudun su ko rashin sa’a ya yi a yayin da wani dan bindigar ya kuma kame shi sa’adda yake gudun tsira.
Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kaduna, Joseph John Hayab, ya ce dan bindigar da ya sace dalibin karo na biyu, ya nemi a biya shi kudin fansa naira 130,000.
Hayab ya ce “wani bawan Allah ne ya kawo mana yara uku da suka kubuto har gida, to amma na hudunsu kam sai da muka biya fansa naira 130,000, bayan da ya kuma fadawa hannun wani dan bindigar.”
Ya kara da cewa “bayan an jima ana tattaunawa da dan bindigar, daga karshe mun je mun nemi kudin muka biya, daga nan kuma ya nemi sai an saya masa karamar wayar salula da layin sim. Mun yi masa dukan wadannan sa’annan muka karbi yaron da misalign karfe 11 na dare.”
A ranar 8 ga watan Yuli ne ‘yan bindiga suka kai hari a makarantar ta Bethel Baptist da ke kudancin Kaduna, inda suka yi awon gaba da dalibai kusan 121.
Bayan sako dalibai 28 daga cikin su, da kuma karin 4 da suka kubuta, shugaban majami’ar Baptist ta Najeriya Reverend Israel Akanji, ya ce har yanzu akwai ragowar daliban makarantar 87 a hannun ‘yan bindigar.