Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Trump a Faransa Ba Ta Sa Ya Sauya Matsayarsa Akan Yarjejeniyar Paris Ba


Shugaban Amurka Donald Trump (hagu) da takwaran aikinsa na Faransa Emmanuel Macron a fadarsa dake Paris, July 13, 2017.
Shugaban Amurka Donald Trump (hagu) da takwaran aikinsa na Faransa Emmanuel Macron a fadarsa dake Paris, July 13, 2017.

Duk da ziyarar da yake yi a Paris dake Faransa, birnin da kasashe 195 suka kulla yarjejeniyar daukan matakan yaki da sauyin yanayi, shugaban Amurka Donald Trump bai nuna wata alama dake nuna zai sauya matsayar da ya dauka kan janye Amurka daga shirin ba.

Har yanzu shugaban Amurka Donald Trump bai yi alkawari canja matsayarsa ta janye Amurka daga cikin yarjejeniyar nan ta Paris ba, wadda ke da nasaba da sauyin yanayi.

Wannan lamari ya zamo wani abu ne da aka ganshi a matsayin banbarakwai domin wannan shine karon farko da ya sa kafa a Paris a jiya alhamis, birnin da aka kulla yarjejeniyar a 2015.

Ganin cewa shugaban Amurka da takwaran aikinsa na Faransa ba su cimma matsaya akan batutuwan da suka danganci sauyin yanayi da kasuwancin ba, ya sa suka mayar da hankulansu kan batutuwan da suka shafi Syria da kuma yaki da ta’addanci.

Mr. Macron, ya ce rashin samun cimma matsayar su ba zai kawo wa ci gaban tattaunawar su cikas ba.

A wuri daya kuma shugaba Trump yana ci gaba da kare ganawar da babban dansa ya yi da wata lauyar kasar Rasha a bara.

Ganawar ta ta'allaka ne akan tayin bai wa dan Trump wasu bayanai akan 'yar takarar jam'iyar Democrat, Hillary Clinton daka iya jefa ta cikin halin ni ‘yasu gabanin zaben da aka yi a bara.

Tun bayan da ya lashe zabe a bara, ake ta takaddama akan cewa Trump ya samu taimakon Rasha a lokacin zaben, zargin da ya ke ta musantawa.

Hillary wacce ta yi wa Democrat takara ita ce suka kara a zaben shugaban kasa da Donald Trump a bara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG