Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Donald Trump Ya Ce Putin Ya So Clinton Ta Ci Zabe


Sabanin rahotannin dake nuna cewa Putin ya taimakawa Trump cin zabe, shugaban na Amurka ya ce Rasha ta so a ce Hillary Clinton ce ta lashe zaben.

Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a jiya Laraba cewa shugaban Rasha, Vladimir Putin zai fi so ace Hillary Clinton ce ta zama shugabar kasa, ba shi ba.

“In da Hillary ce ta ci zabe, da yanzu an gama da dakarun Amurka. Kuma da yanzu duk hanyoyinmu na samun makamashi sun yi muguwar tsada sosai,” a cewar Trump a lokacin da yayi hira da Pat Robertson, wanda ya kirkiro Cibiyar Kafofin Watsa Labarai ta CBN.

Amma Trump ya ce ganawar da yayi da Putin cikin makon da ya gabata a wajen babban taron kasashe masu karfin tattalin arziki da ake kira G20 da aka yi a Jamus, yayi tasiri duk da bam-bamce bambancen da suke da shi.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG