A halin yanzu da ake ci gaba da kai ruwa rana dangane da ‘yan arewacin Najeriya da ake tsare dasu a jihar Abia dake kudu maso gabashin Najeriya, yanzu kuma sai ga wani sabon labari na kama wasu sama da dari biyu a arewa maso gabashin Najeriya.
Wadannan mutane dai a kama sune a kan hanyarsu ta zuwa baga dake cikin jihar Borno kamar yanda shugaban ‘yan asalin tsohowar lardin Sokoto, Alhaji Abubakar Gwandu, ya tabbatarwa wakilimu Haruna Dauda Biu.
Yace mutanen nada alada na zuwa kasar Borno domin noman albasa, a kowace shekara.
Alhaji Abubakar Gwandu ya ummarci hukumomin jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara dasu hana mutanen masu zuwa noma kasar Borno barin jihohinsu a wannan lokaci.