Yau ranar 26 ga watan shida majalisar dinkin duniya ta ware domin fadakarwa akan yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi a duk fadin duniya.
Najeriya na daya daga cikin kasashen duniya da suka dukufa wajen yaki da hada-hadar miyagun kwayoyin musamman a tsakanin matasa. Alhaji Abdullahi Abdul kwamandan hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyin a Najeriya mai kula da jihar Neja ya bayyana mahimmancin ranar.
Yace ranar tana da mahimmanci. Mahimmancin shi ne su tabbatar cewa sun fadakar, sun ilimantar game da illar shan kwaya domin yawancin lokuta wasu suna shiga ba tare da sanin illar miyagun kwayoyi ba. Ba su san illar da ta ke yiwa Danadam ba. A wannan rana sukan hada jama'a su fadakar da su.
Hukumar hana fasakwauri ko kwastan na taka muhimmiyar rawa wajen hana shigowa da miyagun kwayoyi kasar daga kasashen ketare. Maitama Isyaku Kura mai kula da jihohin Kwara, Neja da Kogi ya bayyana irin hobasan da hukumar tasu keyi musamman domin matsayin shugaban kwastan na kasa gaba daya a hukumar kwastan ta duniya.
A Najeriya matasa da dama suna hada-hada da miyagun kwayoyi.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.