Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

RAHOTO NA MUSAMMAN: Hazo-hazon Layi Tsakanin Sojojin Najeriya da Sojojin Haya a Fada da ‘Yan Ta’adan Boko Haram


A garin Mao dake kasar Chadi, dakarun Najeriya na musamman suka yi atisahin kwaikwayon yadda zasu kwato wadanda ake garkuwa dasu. (File Photo)
A garin Mao dake kasar Chadi, dakarun Najeriya na musamman suka yi atisahin kwaikwayon yadda zasu kwato wadanda ake garkuwa dasu. (File Photo)

Garin Maiduguri: A lokacin da wata motar daukan kaya kirar Toyota pik-up ta bayyana a makon jiya a babban titi wajen garin Konduga, garin arewaci maso gabas, nagaba wajen yaki da kungiyar boko haram, an fara da tankar yaki ta rundunar sojojin Najeriya, a kan hanya.

A daidai tsakiyar rana ta ranar goma ga watan Maris, tankar yaki tare da sojojin Najeriya, wadanda suke kokarin kwato garin Bama wanda yake da tazara kadan daga Arewa maso gabas, akwai fargabar cewar dai wata sabuwar hanyar kai hari ce da kungiyar boko haram.

Rundunar sojojin Najeriya sun bude wuta a kan tankar inda suka wargazata, a cewar wasu sojojin Najeriya, wani mashahurin sinadari me suna Hilux, a lokacin da aka kai wannan farmakin a garin Bama. Wasu mutane biyu a cikin wannan motar ta pic-up sojojin sun gayama sashen VOA cewar kodai ‘yan Najeriyane, suka kara da cewar daya daga cikinsu dan kasar Ukrain ne kila ma dukansu biyun, don ga dukkan alamu abokai ne.

Bayan kwanaki shidda sojojin Najeriya suka samu nasarar kwato garin Bama.

Sudai mutane biyun sojojin hayane, wadanda gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta kawo, don kokarin kawo zama lafiya, bayan kwashe shekaru shida ana yaki da ‘yanta’addar boko haram.

Su dai mutun biyun an kashesu ne bisa ga kawance a tsakanin sojojin Najeriya da sauran mayakan. Don kawo karshen mayakan ta’addanci.

Fiye da sojojin haya dari ne ‘yan kasashen Afrika ta kudu, kasar Ukrain, ke yakar wadannan yan ta’addar a yanzu tare da sojojin Najeriya, Anaganin cewar rundunar sojojin Najeriya narike da wadannan yankunan da ‘yan ta’adda ke rike da su a baya.

Duk dai da cewar ana cigaba da samun nasara, ganin zaben shugaban kasa ya rage saura makonni, wannan na iya zama wani abun murna ga mazauna yankin arewa maso gabas. Kila sakamakon zaben na iya kasancewa da ban bisa dalilin wannan nasarar da aka samu da sojojin haya, ba da sojojin Najeriya ba da a ke jiran ganin rawarsu.

An kwato Garin Bama

A lokacin da ‘yan ta’addan kungiyar Boko haram su ka kame garin Bama a watan Satunba, garin Bama shine gari na biyu a girma a jihar Borno, wanda take a Arewa maso gabashin kasar kuma tana makotaka da kasashen Chadi, Nijar, da Camaroon. Mafi akasarin garuruwan wannan yanki mutane dai sun bar mazaunansu bisa tilas.

Sudai wadannan ‘yan ta’addan wadanda ke ikirarin tsaurin addini, da kuma rabuwar kai a siyasance, daga baya sun wallafar da wani bidiyo a yanar gizo, wanda ya nuna suna cin zarafin fararen hula, inda suka sa su suka kwanta a rigirgine.

A farkon shekarar 2015, kungiyar na rike da yanki da ya kai kimanin girman jihar Merilan ta nan Amurka, wanda ya hada da misalign manyan garuruwa a jihar Borno. A watan Janairu, kungiyar suka kwace garin Baga, wanda ke kusa da iyakar kasar Chadi, inda suke rike da matattarar hadin gwiwar sojojin Najeriya da na Chadi, kana da Nijar.

A cewar magabatan rundunar sojojin Najeriya, na ganin kamar sun yanka dubban mutane fararen hula, a lokacin da mutane ke neman wucewa a yankin, tekun Chadi.

A farkon watan Fabrairu, hukumar sojojin Najeriya a sanarda cewar bazasu iya shiga cikin harkar zabe ba saboda rashin tsaro a yankunan, wannan yasa aka dage zabe zuwa 28 ga watan Maris.

Tun bayannan, duk da haka, kambun yakin ya juya, acewar hukumomi lokacin da suka bayyana ma manema labarai har da VOA. Duk mayakan kasar Chad da Camaroon, sunyi rawar gani na kame garuruwa a jihar Borno, wanda suka hada da Damasak, inda ranar Laraba, wanda daruruwan sojoji sukayi ma kawanya a kantituna.

Ranar 10 ga watan Maris, rundunar mayaka sojojin Najeriya ta 7, sun mamaye saman titi a yankin Arewa maso gabashin jihar Borno, sojoji da suka shiga wannan yakin a baya karo na uku wajen kokarin kame garuruwan da suka gayama VOA. Musamman ma saboda maharban boye da kan zauna a saman bishiyoyi.

Abubuwan da mukanyi ko da yaushe muka isa, ko kamin wannan harin, ba kawai bude wuta mukeyi ba na kan me uwa dawabi, da kuma harbi kan bishiya don tsammanin wasu maharban kan makale, a cewar daya daga cikin sojojin, wani me mukamin kopral a cikin mayaka na musamman a sannanin.

Ba tare da samun wani sako daga Toyota ba, sai t-72 suka bude wuta, inda suka lalata motar lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu a cikin motar kirar Toyota.

Wadanda suka mutu sun hada da wani dan kasar Afrika ta kudu da wani dan kasar Ukarien yayin da daya jami’in ya ce dukkaninsu ‘yan kasar Ukraine ne.

“Tankar yakin ta fara da motar mai kiran pick-up ne, kafin su gano cewa abokanansu ne.” in ji shi.

Ya kara da cewa “babu wanda ya san ko su waye, a daidai lokacin da suka tunkaro mu sai tankar yakinmu ta bude wuta. Ba mu san ko su waye ba.”

“Mutane biyu aka kasha,” ya ce. “sun makara, matsalar it ace dakarunmu suna da kayayyakin sadarwa, saboda haka matsalar sadarwa ita ta haifar da wannan hadari.”

A makon da ya gabata, Muryar Amurka ta ruwaito wasu sojojin Najeriya suna cewa lallai akwai wasu dakarun kasashen waje da ke horar da su suke kuma taya su fada da kungiyar Boko Haram, inda a wasu lokuta ma suna tuka jiragenmu masu saukar ungulu.

Hukumomin gwamnatin, har da ma shugaba Goodluck Jonathan sun tabbatar da cewa akwai sojojin haya da aka dauko domin su horar da na Najeriya ba wai su yi yaki da Boko Haram ba.

Daga cikin kasashen Ukraine da Afrika ta kudu babu wanda ya fito fili ya bayyana cewa an kasha dan kasarsa.

Batun ta kasa dakile rikicin Boko Haram ya zamanto babban batu yayin da ake tunkar zabuka a ranar asabar inda abokin hamayyarsa Muhamadu Buhari ya zarge shi da rashin tabuka komai.

“Yadda gwamnatin kasar ta hayo sojoji ya zubar da kimar dakarunmu a idon duniya.” In ji abokin dan takararar Buhari, Yemi Osinbajo a wata ganawa da ya yi da Muryar Amurka.

“Babu yadda za a yi a ce sojojin wadanda suna cikin sojoji kwararru a duniya a ce sai an hayo wasu daga waje.” Ya kara da cewa.

Wannan yaki da kungiyar ta Boko Haram ya na kuma samun cikas saboda babu hadin kai da tsara abubuwa yadda ya kamata tsakanin dakarun kasa da na sama in ji jami’in.

“Wasu lokuta mu kan kira sojojin sama mu gaya musu inda ‘yan Boko Haram su ke amma kuma sais u ce mana sun je bas u ga kowa ba, sai su ce mu je mu yake su da kanmu.” Ya ce.

“Hakan ne yasa aka yanke shawarar a baiwa dakarun kasar waje jiragen, saboda haka wadannan tsoffin sojojin su ne suke tuka jiragen.”

A ranar 16 ga watan Maris, dakarun Najeriya suka bayyana cewa sun kwato garin Bama.

“Ina mai farin cikin gaya muku cewa rundunar soji ta 7 ta sojojin Najeriya sun kwato garin Bama a wannan rana a daidai lokacin da dakarun hadin gwiwa ke da suka hada da na Chadi da da Nijar suka kwato garin Damasak da Mobbar dukkaninsu a jihar Borno.” In ji wani sojan Najeriya Kanar SK Usman a wata sanarwa.

Daga baya da Muryar Amurka ta yi kokarin tintibi Usman domin karin bayani kan ko akwai wadanda suka jikkata da kuma Karin bayani kan yawan masu ta da kayar da aka kasha sai ya ki ba da hadin kai.

XS
SM
MD
LG