Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Dalibai Kusan 100 Suka Suma A Lokacin Rubuta Jarabawa A Jihar Ekiti


Kwamishinan Lafiya na jihar Ekiti, (dama) Oyebanji Filani lokacin da yake kai wa daliban ziyara a asibiti (Twitter/ Ekiti Ministry of Health)
Kwamishinan Lafiya na jihar Ekiti, (dama) Oyebanji Filani lokacin da yake kai wa daliban ziyara a asibiti (Twitter/ Ekiti Ministry of Health)

Daliban Kwalejin Kiwon Lafiya da Fasaha, da ke Ijero-Ekiti a ranar Laraba sun yi zanga-zanga bayan da abokan karantunsu su kimanin 100 suka suma sanadiyyar shakar wani sinadari.

Rahotanni na cewa daliban sun fadi ne yayin rubuta jarabawarsu bayan shakar sinadarai a lokacin da jami'an hukumar kashe gobara ta tarayya ke aikin gwaje-gwaje.

Bayanai sun yi nuni da cewa wasu daga cikin daliban da aka kwantar a asibitin suna da cutar asma ne kuma sun samu matsala sakamakon sunadarin da suka shaka yayin aikin gwaje-gwajen.

Dalilin haka ya sa ɗaliban suka fusata, nan-da-dan suka taru kuma suka kewaye sashin gudanarwa na makarantar don neman bayani daga hukumomin makarantar.

Zanga-zangar daga baya ta rikide ta zama tashin hankali yayin da aka lalata ginin makarantar, dakunan laccoci, motocin malamai da sauran kadarori na miliyoyin aka lalatasu, hakan ya tilasta wa malamai da sauran ma’aikatan suka gudu.

Kwamishinan lafiya na jihar Ekiti, Oyebanjo Filani (Hagu) yana ganawa da jami'an kwalejin (Twitter/Ekiti Ministry of Health)
Kwamishinan lafiya na jihar Ekiti, Oyebanjo Filani (Hagu) yana ganawa da jami'an kwalejin (Twitter/Ekiti Ministry of Health)

Tuni dai ma'aikatar lafiya a jihar ta Ekiti, wacce ke kudu maso yammacin Najeriya, ta tabbatar da ukwar wannan lamari, inda ta ce adadin daliban da aka kwantar a asibiti sun kai 36.

Karin bayani akan: daliban, jihar Ekiti, Zanga-zangar, Nigeria, da Najeriya.

"Kusan dalibai 100 abin ya shafa, amma a lokacin da kwamishinan lafiya Oyebanji Filani ya kai ziyara makarantar, dalibai 36 aka kwantar a asibiti." Ma'aikatar lafiyar jihar ta ce.

Ta kara da cewa, an kai biyu daga cikin daliban 36 zuwa asibitin koyarwa na Afe Babalola don samun karin kulawa.

"Muna masu bakin cikin faruwar wannan al'amari, mun kuma sa ido akan daliban da ke kwance a asibiti., don mu tabbatar sun samu sauki."

Hukumomin jihar sun kara da cewa, lamarin ya faru ne saboda wani feshin maganin ciyawa da aka yi a makarantar, wanda ta kwatanta a matsayin wanda "ba a yi shi a lokacin da ya dace ba."

XS
SM
MD
LG