Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum Miliyan 1.8 Ne Za Su Tsere Daga Sudan Nan Da Karshen Shekara - MDD


‘Yan gudun hijira daga kasar Sudan
‘Yan gudun hijira daga kasar Sudan

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin ta bukaci dala biliyan 1 don taimaka wa wadanda ke gudun hijira a Sudan, inda ta ce tana sa ran sama da miliyan 1.8 za su tsere zuwa kasashe makwabta biyar a karshen shekara.

WASHINGTON, D.C. - Kiyasin da aka yi yanzu ya kai kusan ninki biyu abin da UNHCR ta yi hasashe a watan Mayu jim kadan bayan barkewar rikici.

Iyakokin Sudan
Iyakokin Sudan

Tuni dai sama da mutum miliyan 1 suka tsere daga Sudan zuwa wasu jihohin da ke makwabtaka da su, sakamakon fadan da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun gaggawa na RSF a babban birnin kasar na Khartoum da kuma wajen kasar.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG