Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bangarorin Dake Yaki Da Juna A Sudan Na Nuna Rashin Kulawa Ga Fararen Hula


'Yan Gudun Hijrar dake tserewa fadan Sudan.
'Yan Gudun Hijrar dake tserewa fadan Sudan.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun ce bangarorin da ke rikici da juna a Sudan suna nuna rashin kulawa ga fararen hula a yammacin Darfur, daya daga cikin jigon yakin basasar Sudan.

Henry Wilkins ya yi magana da 'yan gudun hijira a Borota na kasar Chadi, wadanda suka yi nasarar tserewa daga yankin amma ya ce kungiyoyin da ke dauke da makamai suna kai hari, da muzgunawa wasu lokutan kuma suna hana wasu ficewa.

Ali Abed Allah Yakoub, dan gudun hijirar Sudan, ya ce dansa mai shekaru 32 a duniya ya makale a Geneina, babban birnin lardin Darfur ta Yamma, a tsakiyar yakin basasar Sudan.

A wani faifan bidiyo da wani dan jarida dan kasar Sudan ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya nuna yadda ake gwabza fadan. Rahotannin da ke da wuya a iya tantancewa saboda rashin damar shiga birnin, sun ce kila an kashe daruruwan mutane a fadan da aka gwabza a karshen mako.

Da yawa daga cikin ‘yan gudun hijirar Sudan da Muryar Amurka ta zanta da su a Chadi, sun ce an bar su da wani zabin da ba zai taba yiwuwa ba, su zauna a Geneina cikin tashin hankali ko kuma su jajirce kan hanyar zuwa Chadi, inda kungiyoyi masu dauke da makamai za su iya kai musu hari ko kuma su kashe su.

Wata 'yar gudun hijira, wacce ta ki bayyana sunanta saboda tsoron tsaron danginta, ta ce ta bar 'yan uwa a Geniena saboda haka.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce dukkan bangarorin biyu a yakin Sudan, na nuna rashin kula da rayukan fararen hula ta hanyar amfani da ababen fashewa don lalata wuraren al’umma da asibitoci.

Sun kuma ce duk da haka mutane na fargabar ficewa.

A makon da ya gabata ne aka cimma yarjejeniya tsakanin sojojin Sudan da ke rikici da kungiyar dakarun sa kai na RSF, domin ba da dama ‘yan gudun hijirar dake ficewar daga Sudan su tsallake lafiya. Sai dai an ci gaba da gwabza fada, kuma har yanzu akwai karancin damar fita daga kasar cikin sauki.

XS
SM
MD
LG