Idan an tuna dai tun daga ranar Litini da ta gabata aka kafa wannan dokar ta hana fita bayan da wasu 'yan bindigar da ake kautata zaton 'yan kungiyar nan ce ta Jama'atu Ahlissunnah Lid Daawati wal Jihad, wadda ake wa lakabi da Boko Haram. To amma dokar ba ta shafi ma'aikatan asibiti da 'yan kwana-kwana da 'yan jarida da sauran wadanda aka fai bukatar ayyukansu a yanayi irin wannan.
Wakilinmu a jihar ta Borno, Haruna Dauda Biu, ya ce wasu mutanen da su ka fito sabanin dokar sun sha bulala da kuma tsallen kwado. Haruna Dauda ya kuma ce Gwamnan jihar ta Borno Hon Kashim Shatima bai wa 'yan hijar hakuri saboda mawuyacin halin da aka fada. Amma, in ji Haruna, tuni ma wayoyin tafi da gidanka su ka fara aiki a wasu sassan birnin Maiduguri.
.