Yayin da musulmi ke haraman fara azumin watan Ramadan, da alamu dai kungiyoyi sun fara amsa kiran da akeyi na a taimaka wayan gudun hijiran da rikicin boko haram ya raba da gidajen su da kuma masu karamin karfi a cikin al’umma.
Domin amsa wannan kiran ne ma kungiyar Izalatul bidiaa waikamatus sunna (JIBWIS) ta kaddamar da wata gidauniyar tallafa wa wadannan yan gudun hijiran alfarman wannan watan na azumi.
Sheik Abdullahi Bala Lau da yake shugaban kungiyar a Najeriya ya bayyana muhimmancin irin wannan gidauniyar.
‘’Ba shakka mun tura wadanda wannan masifa na Insugency ya same su, a Borno, Adamawa, da kuma Taraba gudun mowa, hakanan kuma tunda muna fuskantar watan Ramadan akwai shirye-shirye na musammam domin sake duba wadanda zamu iya tallafawa amma m un bada umurni ko wace jiha suyi kokari yan gudun hijiran dake wannan jiha a karkashin wannan kungiyar ta mu ta Izalatul Bidia Waikamatus Sunna an nemi gudun hijiran da za a iya kaiwa gay an gudun hijira da suke wannan jiha kamar yadda ainihin yadda ake tallafawa marayu fatan shine insha ALLAHU yan gudun hijira da hursunino ma a gidajen yari da marayu zasu gane cewa an shiga watan azumin Ramadan kuma muna addua subanahu wata ala ya kawo sauki’’.
Kamar kungiyar ta Izala ita ma kungiyar ta Mujumau Ahababun Rasullahi tayi wa azumin bana tanadi kamar yada wani jamiin kungiya a jihar Taraba Alhaji Habibu Hassan Almaki ke cewa.
‘’Yawaita alheri dukkan kungiyoyin da ake dasu kowa yayi kokarin yaga an taimakawa mutane mara sa galihu’’.
An tambaye shi ko su me zasu yi a jihar Taraba? Shine sai yace
‘’To Taraba dai mun saba gabatar da karatuttuka da abinda za a taimaka wa ainihin bayin ALLAH na harkan sayen hatsi gero, kuma ayyukan mu Kenan mu kira bayin ALLAH a rika ba bayin ALLAH sadaka wannan shine aikin mu’’
To sai dai tashin kayan masarufi idan lokacin azumi yazo nama cikin matsalolin da akan koka to ko wane tanadin yan kasuwan suka yi a bana?
Wakilin muryar Amurka Ibrahim Abdul Azeez ya ziyarci kasuwar gwari ga kuma zantawarsa da wani dan kasuwa.
Ina sunan ka kukma me kake sayarwa anan?
‘’Sunana Sulemam BZ, muna sayar da kankana da kuma lemu da abarba da ayaba, tanadin da muka yiwa azumin bana shine musali a azumin da ya wuce abubuwa sunyi tsada amma bana in ALLAH ya yarda abubuwan zasu yi sauki kamar lemu da ayaba da kankana da abarba in ALLAH ya yarda abin zaiyi sauki ba kamar na bariya wanda ya wuce ba’’ .
Kamar dai yan lemu suma yan gwarin kayayyakin abin miya sunyi alwashin sauke farashi a bana.
‘’Na farko dai sunana Abdullahi Tijjani state chairman na Gwari Traders Association Taraba State ba wani tsari da muka yi wai muga kayan gwari yayi tsada zamu yi hubbasa dai muga mun shiga mun fita duk inda wannan kaya yake muga munkwakulo shi saboda ansa harkan azumi hark ace wadda aka fi anfani dashi kowane bil adam da yake azumi yafi son yaga yaci jan miya’’.
Yanzu ma dai tuni aka fara wanke masallatai domin yiwa azumi matrhabin wanda za afara a kasa da awoyi 72.